Za a samu gagarumin ci gaba sosai a lamarin tsaro a wannan shekarar, Buhari

Za a samu gagarumin ci gaba sosai a lamarin tsaro a wannan shekarar, Buhari

- Gwamnatin tarayya ta sha alwashin kawo gagarumin ci gaba a harkar tsaron kasar cikin shekarar nan

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya tabbatar da hakan a wajen bikin tunawa da ranar sojoji

- Ya kuma yi jinjina tare da addu'a ga dakarun sojin da suka rasa ransu wajen yi wa kasarsu hidima

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce kasar za ta samu gagarumin ci gaba a lamarin tsaro a 2021.

A wasu jerin wallafa da yayi don raya ranar tunawa da sojoji, Shugaban kasar ya bukaci shugabannin tsaro da su tabbatar da hada hannu wajen yaki da rashin tsaro.

Buhari ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da ba jin dadin rundunar sojin muhimmanci.

Za a samu gagarumin ci gaba sosai a lamarin tsaro a wannan shekarar, Buhari
Za a samu gagarumin ci gaba sosai a lamarin tsaro a wannan shekarar, Buhari Hoto: @Buharisallau1
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Rundunar yan sanda ta sake rashin AIG na biyu cikin kwanaki 3

“Yayinda muke raya ranar tunawa da sojoji, bari na nuna jinjina ga jarumta da sadaukarwar dukkan maza da matan rundunar sojinmu wadanda suka sadaukar da rayuwarsu don hadin kanmu, zaman lafiya da tsaronmu. Muna kuma jinjina ga dakarunmu wadanda a yanzu suke kan gaba a ayyukan tsaron cikin gida,” Buhari ya rubuta.

“Jin dadi da kula da lafiyar dakarunmu zai ci gaba da zama abu mai muhimmanci. Muna zuba jari sosai ba wai a makamai da kayan amfaninsu ba kawai, sai dai harda sama masu muhalli, cibiyar lafiya da sauran abubuwan jin dadinsu. Kuma za mu ci gaba da samar da kayayyaki.

“Ina kara jadadda umurnina ga shugabannin tsaro game da hada hannu da kai sosai, da kuma mayar da hankali ga taron sirri da fassara. Ina da karfin gwiwar cewa za mu ga gagarumin ci gaba a lamarin tsaronmu a wannan shekarar.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Kaduna ta ce ta ceto yaran Almajirai 160 a Kaduna

“Allah ya ji kan jarumanmu da suka rasa ransu. Za mu ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da ganin cewa sadaukarwarsu a madadinmu bai tafi a banza ba."

A wani labarin, bayan shirye-shiryen karban bashi domin biyan albashi da yin wasu ayyuka dake cikin kasafin kudin 2021, gwamnatin tarayya ta tabbatar da jita-jitan cewa za ta sayar da wasu dukiyoyin gwamnati yanzu.

Gwamnatin ya kara da cewa za'a yi amfani da wasu dukiyoyin da ba na man fetur ba domin daukan nauyin kasafin kudin 2021.

Hakan na kunshe cikin takardar da ministar kudi, Zainab Ahmed, ta gabatar ga masu ruwa da tsaki kan kasafin kudin 2021 da shugaban kasa ya rattafa hannu, Premium Times ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel