Gwamnatin Kaduna ta ce ta ceto yaran Almajirai 160 a Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta ce ta ceto yaran Almajirai 160 a Kaduna

- Gwamnatin jihar Kaduna ta kai samame tare da ceto yaran Almajirai 160

- Hakan na daga cikin kokarin da kwamitin yaki da annobar korona ta jihar ke yi don dakile yaduwarta

- Hadimin Gwamna Nasir El-Rufai, Muyiwa Adekeye ne ya tabbatar da hakan a ikin wata sanarwa da ya fitar

Gwamnatin Kaduna ta bayyana cewa ta ceto yaran Almajirai guda 160 daga makarantu da gidajen da basu dace ba a jihar.

Gwamnatin jihar ta ce wasu daga cikin yaran sun fito ne daga jihohi 13 a yankin arewa da kudancin kasar yayinda sauran suka fito daga Jumhuriyar Benin, Burkina Faso da kasar Nijar.

Tsarin karatun Almajiranci shine inda yara ke barin gidajensu zuwa nesa don neman ilimin addinin Musulunci.

Gwamnatin Kaduna ta ce ta ceto yaran Almajirai 160 a Kaduna
Gwamnatin Kaduna ta ce ta ceto yaran Almajirai 160 a Kaduna Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

A wata sanarwa da ya saki a ranar Juma’a, 15 ga watan Janairu, Muyiwa Adekeye, mai bayar da shawara na musamman ga gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, ya ce wuraren da aka samu yaran ya saba ma tsarin da jihar ta kafa.

KU KARANTA KUMA: Daukar ma’aikata: Farin ciki fal yayinda wani gwamna ya amince da daukar matasa 4,000 aiki

Wani bangare na sanarwan ya ce:

“Jami’an kwamitin yaƙi da annobar korona ta jihar Kaduna sun ceto yara 160 daga wuraren da basu da izini da lasisin zama makaranta ko a matsayin gidajen yara,' in ji Adekeye.

“Ajiye yaran a wuraren da babu izini, wuraren kuma sun saba dokar amfani da fili na gwamnatin Kaduna da manufar mayar Almajirai jihohinsu da kananan hukumominsu domin ci gaba da karatunsu a karkashin kulawar iyayensu, da kuma makarantu masu rijista.

“KDSG na fatan tunatar da dukkanin kungiyoyi, gidauniya, shugabannin addini da makarantun addini cewa gwamnatin jihar na da dokoki da ke wajabta karatun dukkan yara a makarantu masu rijista.”

Kakakin ya ce tun a ranar 31 ga watan Maris, 2020 aka fara mayar da yaran Almajirai jihohinsu na ainahi.

“Tuni gwamnatin Kaduna ta dauki wani tsari ma ci gaba don gano wuraren da aka ajiye wadannan yara da kuma daukan matakan ceto su daga irin wadannan wurare da kuma sada su da iyayensu don ci gaba da karatunsu,” in ji shi.

“Daga cikin kokarin da ake na aiwatar da wannan manufar, jihar Kaduna ta karbi yara 1,118 daga jihar wadanda aka dawo da su daga wasu jihohi.'

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Rundunar yan sanda ta sake rashin AIG na biyu cikin kwanaki 3

“Yaran da aka tabbatar yan jihar Kaduna ne za a mika su zuwa kananan hukumominsu na usuli sannan a mika su ga jami’an karamar hukuma don yi musu rijista da tura su makarantu a karkashin kulawar iyayensu.

“Yaran da suka fito daga kasashen ECOWAS, za a mika su ga hukumar kula da shige da fice ta Najeriya don daukar matakan da suka dace."

Adekeye ya kara da cewa ya kamata al’umma su dauki alhakin kula da tarbiyar yaransu, jin dadinsu da kuma dawainiyarsu.

A baya mun ji cewa Gammayar jami'an tsaro sun kai sumame gidan Shaihi Dahiru Usman Bauchi na Jihar Kaduna sun kwashe masa almajirai.

Fatahu Umar Pandogori, shugaban makarantun Dahiru Bauchi na Kaduna da kewaye Kaduna ya tabbatar da afkuwar lamarin.

Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce nan bada dade wa ba za ta fitar da karin bayani game da lamarin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng