Zazzafan martani daga yan Nigeria yayinda Buhari ya saki tantabaru amma suka ki tashi a wajen tunawa da sojoji

Zazzafan martani daga yan Nigeria yayinda Buhari ya saki tantabaru amma suka ki tashi a wajen tunawa da sojoji

- Bikin ranar tunawa da sojoji a Najeriya na 2021 na tashe a shafukan soshiyal midiya da wani sabon salo

- A wajen bikin, Shugaba Buhari ya saki wasu tantabaru a sama, kamar yadda yake bisa al’ada

- Sai dai, tantabarun sun ki tashi sama, lamarin da ya haddasa zazzafan martanin daga yan Najeriya a shafin soshiya midiya

Yayinda Najeriya ke bikin ranar tunawa da rundunar soji na 2021 a ranar Juma’a,15 ga watan Janairu, wani abun al’ajabi ya faru inda ya haddasa zazzafan martani daga yan Najeriya a shafin soshiyal midiya.

Kamar yadda yake bisa al’ada, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bude kejin tsuntayen, sai ya dauki daya daga cikin tantabarun ya jefa a sama amma sai ya sauka a sama kejin ya ki tashi.

Shugaban kasar ya bude sama kejin a kokarinsa na fitar da dukkansu amma sai tantabarun suka ki tashi, lamarin da yasa dole Shugaban kasar ya koma mazauninsa.

Zazzafan martani daga yan Nigeria yayinda Buhari ya saki tantabaru amma suka ki tashi a wajen tunawa da sojoji
Zazzafan martani daga yan Nigeria yayinda Buhari ya saki tantabaru amma suka ki tashi a wajen tunawa da sojoji Hoto: @paschal2k2
Asali: Twitter

Koda dai wasu daga cikin tantabarun sun tashi daga bisani lokacin da shugaba Buhari ke komawa mazauninsa, rashin tashin tantabarun a lokacin da Shugaban kasar ya sake su ya janyo cece-kuce a shafukan soshiyal midiya.

Legit.ng ta tattaro martanin yan Najeriya kan lamarin:

Thεό Abu, @TheoAbuAgada, ya ce:

“Mun gode faaa tantanbaru.

“Bamu san cewa za ku iya sanar da wadanda ke mulki yadda muke jib a kamar yadda kuka yi a yanzu.”

SEGA L'éveilleur, @segalink, ya ce:

“Me zai sa ku bijire ku tantabaru?! Ya zama dole a rike jam’iyyun adawa a kan kin tashin wadannan jakadu na zaman lafiya. Muna baka hakuri ya Shugaban kasa, kada ka kula su. Ya zama dole a binciki tantabarun sannan a gano wadanda suka hada kai da su. Aikin banza.”

Pastor Ola, @Biisi96, ta ce:

“Tsuntsaye na son tashi.

“Tsuntayen keji na tashi da zaran an bude su.

“Mutumina ya bude keji, harma yayi kokarin tura tantabarun don su tashi. Amma suka ki yarda.

“Tantabaru basa so yan bindiga su kama su, a ina papa tantabara zai ga 4M a wannan lokaci na bazara.”

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce kasar za ta samu gagarumin ci gaba a lamarin tsaro a 2021.

A wasu jerin wallafa da yayi don raya ranar tunawa da sojoji, Shugaban kasar ya bukaci shugabannin tsaro da su tabbatar da hada hannu wajen yaki da rashin tsaro.

Buhari ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da ba jin dadin rundunar sojin muhimmanci.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel