Budurwa ta rasu kwanaki biyar kafin daura mata aure

Budurwa ta rasu kwanaki biyar kafin daura mata aure

- Budurwa ta rasu a hatsarin mota kwanaki biyar kafin a daura mata aure da saurayin ta

- Petra Nji tare da Isbias Forsack, wadda zata aura suna hanyarsu ta dawowa daga daukan hoto ne suka yi hatsari

- Forsack da sauran fasinjojin motar sun jikkata an garzaya da su asibiti amma Nji ta ce ga garinku

Wata budurwa yar kasar kamaru da ke karatun zama ma'aikaciyar jinya, Petra Nji ta rasu a hatsarin mota kwanaki biyar kafin a daura mata aure.

Petra da mijin da za ta aura, Isbias Forsack suna hanyarsu ta dawowa daga Douala ne bayan zuwa daukan hotunan kafin aurensu inda hatsarin ya ritsa da su a kan titin Tiko-Douala a ranar Litinin, 11 ga watan Janairun 2021.

Budurwa ta rasu kwanaki biyar kafin daura mata aure
Budurwa ta rasu kwanaki biyar kafin daura mata aure. Makongho Fossong Gissela
Asali: Twitter

Budurwa ta rasu kwanaki biyar kafin daura mata aure
Budurwa ta rasu kwanaki biyar kafin daura mata aure. Makongho Fossong Gissela
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Dukkanku dajin Sambisa za ku garzaya, Buratai ga sojin da ake horarwa

Isbias da sauran fasinjojin da ke cikin motar sun samu raunuka daban-daban kuma an garzaya da su zuwa wani asbiti da ke kusa amma ita Petra ta mutu.

An shirya yin auren su na coci ne a ranar Asabar 15 ga watan Janairu a cocin Presbyterian da ke Molyko yayin da auren gargajiya kuma za a daura a ranar Juma'a 15 ga watan Janairu.

KU KARANTA: Mutumin da budurwarsa ta cinnawa wuta a Benue ya mutu

Wasu kawayen amaryar sun sanar da rasuwarta a shafinsu na dandalin sada zumunta na Facebook inda suka yi mata addu'ar samun rahamar Ubangiji tare da yi wa yan uwanta ta'aziyyar rasuwarta.

A wani labarin daban, kun ji kungiyar samari masu kishin aljihunsu da ake kira Stingy Men Association (SMAN) a turance tana samun bunkasa inda ake ta bude rassa a kasashen duniya daban-daban, BBC Hausa ta ruwaito.

A ranar Litinin 11 ga watan Janairu ne kungiyar ta bude shafinta na musamman a kafar Twitter da Facebook tare da tamburi a Najeriya.

Wasu kasashen Afirka sun bi sahun Najeriya sun bude rassan kungiyar a kasashensu, kasashen sun hada da Ghana, Liberia, Uganda, Malawi da Zambia.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel