Mutumin da budurwarsa ta cinnawa wuta a Benue ya mutu

Mutumin da budurwarsa ta cinnawa wuta a Benue ya mutu

- Wani mutum ya mutu awanni kadan bayan budurwarsa ta babbake a Jihar Benue

- Rundunar yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin tare da bayyana cewa tuni suka kama mai tabargazar

- Tuni iyalan mamacin suka dauki gawar sa daga asibiti don yi masa sutura

Wani mai siyar da magani, Chidinma Ikechukwu Omah, wanda budurwarsa ta cinnawa wuta a rukunin shagunan Wadata a Makurdin Jihar Benue ya rasu, The Nation ruwaito.

Omah wanda aka ruwaito ya rasu da misalin karfe 10:00 na daren Litinin sanadiyar mummunar konewar da yayi bayan budurwarsa, Esther Alex, ta zazzaga masa fetur tare da cinna masa ashana da misalin karfe 2:00 na ranar Litinin din.

Mutumin da budurwarsa ta cinnawa wuta a Benue ya mutu
Mutumin da budurwarsa ta cinnawa wuta a Benue ya mutu. Hoto: @MobilePunch
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Dukkanku dajin Sambisa za ku garzaya, Buratai ga sojin da ake horarwa

Mai magana da yawun hukumar yan sandan Benue, DSP Catherine Anene, ta tabbatar da faruwar lamarin ga wakilin mu a Makurdi.

Anene ta kuma tabbatar da kama Esther wadda tuni ta na tsare a hannun rundunar.

KU KARANTA: Mai garkuwa ya biya N1.5m don fansar kansa daga hannun 'yan bindiga da suka sace shi

A daya bangaren, tuni iyalan mamacin suka dauke gawar sa daga Federal Medical Centre da ke makurdi don binne shi.

A wani labarin daban, rikici ya kaure a zauren majalisar Jihar kasar Ghana a jiya Laraba 6 ga watan Janairu bayan rushe majalisar kunshi ta bakwai.

A cikin hoton bidiyon da ya karade shafukan dandalin sada zumunta, an gano rikici ne ya kaure tsakanin yan jam'iyyar NPP da NDC kan wacce jam'iyya ne ke da rinjaye kuma wacce zata fitar da sabon Kakakin Majalisa.

Kamar yadda bidiyon ya nuna, wasu daga cikin yan majalisar sun rika kai wa juna hannu sannan wasu suka rika fatali da akwatunan kada kuri'a da ke zauren majalisar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel