Sallamar hafsoshin tsaro: Mutane basu hango abinda Buhari yake hange, Garba Shehu

Sallamar hafsoshin tsaro: Mutane basu hango abinda Buhari yake hange, Garba Shehu

- Mataimaki na musamman ga Shugaban kasa Buhari, Malam Garba Shehu ya ce 'yan Najeriya basu hango abinda Buhari ke hange

- Ya yi wannan zancen ne bayan da aka tambayesa dalilin da yasa shugaba Buhari ke cigaba da aiki da hafsoshin tsaro har yanzu

- Ya kara bayyana cewa mukaminsu ba mai wa'adi bane, hakkin kuma shugaban kasa ne sauya su amma ya nuna gamsuwarsa da su

Garba Shehu, babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan yada labarai, ya ce shugaban kasa bai sallami shugabannin tsaro ba ne saboda yana hango wata nagartarsu da 'yan Najeriya basu gani.

Shehu ya sanar da hakan a wani bakuncinsa da TVC ta karba kuma jaridar Vanguard ta ruwaito.

A yayin martani ga tambayar da aka yi masa a kan abinda ya hana Buhari ya sallami shugabannin tsaro duk da yadda ake ta bukatar yayi hakan, Garba ya ce:

Sallamar hafsoshin tsaro: Mutane basu hango abinda Buhari yake hange, Garba Shehu
Sallamar hafsoshin tsaro: Mutane basu hango abinda Buhari yake hange, Garba Shehu. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

KU KARANTA: Hotunan direbobin tifa suna toshe babbar hanyar Gusau zuwa Sokoto, sun sanar da dalili

"Saboda yana ganin abinda masu caccaka basu gani. Yana ganin abinda mutane da yawa basu gani.

"Ba nadi bane mai wa'adi. Babu wata doka da tace sai shugabannin tsaro an sallamesu bayan sun kwashe shekaru biyu.

"Suna aiki ne da gamsuwar shugaban kasa. A yanzu kuwa shugaban kasan ya ce zai yi gyaran. Toh ya rage gare shi ne kawai. Ina tunanin ya dace 'yan Najeriya su bada uziri."

A bangaren yaki da kungiyar ta'addanci ta Boko Haram, Garba ya ce:

KU KARANTA: 'Yar bautar kasa ta sha duka, an yi mata tumbur bayan kashe saurayin da ta kwana da shi (Hotuna)

"Kasar nan tuntuni ta kasance da kalubalen rashin tsaro. Babu kasar da babu masu laifi. Kullum sauya salo kalubalen suke amma ana kokarin ganin bayansu.

"Daga abinda shugaban kasa yace, 2021 ba za ta yi wa 'yan Boko Haram, 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane dadi ba."

A wani labari na daban, 'yan majalisar Amurka sun fara shirye-shiryen tsige Donald Trump daga kujerar shugabancin Amurka a ranar Litinin.

Sun zargi shugaban kasar da tayar da tarzoma a babban birnin Amurka. Sannan sun zarge shi da janyo tashin hankali da rikici, da kuma yin ikirari marasa dadi akan zaben shugaban kasa da aka yi.

Sun bukaci mataimakin shugaban kasar, Mike Pence da ya yi amfani da gyararriyar doka ta 25 a kundin tsarin mulkin Amurka don ya amshi mulki daga hannun Trump.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel