Hotunan direbobin tifa suna toshe babbar hanyar Gusau zuwa Sokoto, sun sanar da dalili
- A jiya Lahadi ne direbobin tifa suka rufe babbar hanyar Gusau zuwa Sokoto
- Kamar yadda direbobin tifa suka sanar, sun zargi jami'an tsaro da kama mambobinta
- Hukumar NSCDC ta tabbatar da cewa direbobin na hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba
Direbobin tifa a ranar Lahadi sun rufe babbar hanyar Gusau zuwa Sokoto bayan zargin kama mambobinsu da jami'an tsaro suke yi, TVC News ta wallafa hakan.
Wannan matakin da direbobin tifan suka dauka ya tsayar da motoci masu kaiwa da kawowa a Gada biyu na fiye da sa'o'i biyu a babbar hanyar.
Kungiyar na zargin jami'an NSCDC da cutar dasu matuka na kusan watanni shida.
KU KARANTA: Nasara daga Allah: Bidiyon sojin sama suna ragargaza shugabannin Boko Haram
Shugaban kungiyar wanda NSCDC ta gayyata domin amsa tambayoyi, ya ce jami'an NSCDC dauke da makamai ke tsare motocinsu da na wasu direbobi a kan zarginsu da take da hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba.
Kamar yadda yace, babu daya daga cikin mambobinsu da ke da hannu a cikin hakar ma'adanai.
A yayin martani, mataimakin kwamandan NSCDC na jihar Zamfara, Abba Shehu ya ce an kama su ne sakamakon hannunsu a cikin hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba.
Kamar yadda yace, ma'aikatar ma'adanai ta tarayya ce ta sanar da hukumarsu cewa akwai mambobi a kungiyar direbobin tifa da ke da hannu a hakar ma'adinan.
KU KARANTA: Bidiyon 'yar majalisa matar aure ɗare-ɗare a cinyar dan majalisa ya janyo cece-kuce
A wani labari na daban, gwamnatin jihar Akwa Ibom ta sanar da rasuwar tsohon shugaban sojin sama, Air Marshal Nsikak Eduok, Daily Trust ta wallafa.
Eduok tsohon shugaban ma'aikatan sama ne kuma ministan sufurin jiragen sama kuma mutuwarsa tana zuwa ne bayan kwwanaki kadan da rasuwar Air Commodore Nkanga mai ritaya.
Kamar yadda takardar ta fito sanye da hannun sakataren gwamnatin jihar, Dr Emmanuel Ekuwem a ranar Alhamis, Eduok ya rasu a ranar Laraba, 6 ga watan Janairun 2021 bayan fama da ciwon koda da yayi.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng