'Yar bautar kasa ta sha duka, an yi mata tumbur bayan kashe saurayin da ta kwana da shi (Hotuna)

'Yar bautar kasa ta sha duka, an yi mata tumbur bayan kashe saurayin da ta kwana da shi (Hotuna)

- Bidiyon wasu samari suna dukan wata budurwa, inda suka yi mata tsirara, ya karade shafukan sada zumuntar zamani

- Budurwar, wacce mai bautar kasa ce a jihar Akwa Ibom, ta sha duka da zagi, yayin da samarin suke zarginta da kashe wani saurayi da ya kwana da ita

- Ana zargin budurwar da kashe saurayin ne a dakinsa, yayin da tace yayi yunkurin yi mata fyade, amma kowa yayi ta musanta hakan

Wata matashiya mai bautar kasa a jihar Akwa Ibom ta sha duka kamar bakuwar karya a ranar Lahadi. Baya ga dukan, har tsirara wasu samari suka yi mata, suna zarginta da kashe wani mutum bayan ya kwana da ita.

An ga bidiyon matashiyar, mai suna Odume Paschaline, ta kammala karatunta a jami'ar Najeriya dake Nsukka, tsirara haihuwar uwarta, maza suna dukanta da kuma zaginta. Alamu sun nuna a tsakar anguwa ne al'amarin ya faru.

A wani bidiyo da aka tura wa Premium Times ta WhatsApp, wanda wani mutum da lamarin ya faru gaban shi ya kwashe tas a wayarsa, an ga yadda samarin suka tozarta budurwar.

'Yar bautar kasa ta sha duka, an yi mata tumbur bayan kashe saurayin da ta kwana da shi (Hotuna)
'Yar bautar kasa ta sha duka, an yi mata tumbur bayan kashe saurayin da ta kwana da shi (Hotuna). Hoto daga Godwin George
Source: Facebook

KU KARANTA: Boko Haram sun kashe mutum 3, sun yi awon gaba da dabbobi a kusa da Maiduguri

Bayan 'yan sanda sun isa wurin ne suka ceci matar, inda suka tafi da ita a motarsu.

An ga hotunan wanda aka kashe male-male cikin jini a dakinsa. Mutane sun taru a anguwar suna tattaunawa akan yadda za su bullo wa lamarin.

'Yar bautar kasa ta sha duka, an yi mata tumbur bayan kashe saurayin da ta kwana da shi (Hotuna)
'Yar bautar kasa ta sha duka, an yi mata tumbur bayan kashe saurayin da ta kwana da shi (Hotuna). Hoto daga Godwin George
Source: Facebook

Wata majiya ta tabbatar da cewa matar tana hannun 'yan sanda, kuma tayi ikirarin ya yi yunkurin yi mata fyade ne, shiyasa tayi kokarin ceton kanta da kanta.

Kamar yadda majiyar tace, "Budurwar har gidan saurayin taje, da kamar a gidanta ne lamarin ya faru da da sauki."

Sai dai, an ga yadda Paschaline ta kwatanta kanta a shafinta na Facebook, inda tace lallai tana da zuciya mai kyau, amma bata daukar shirme komai kankantarsa.

'Yar bautar kasa ta sha duka, an yi mata tumbur bayan kashe saurayin da ta kwana da shi (Hotuna)
'Yar bautar kasa ta sha duka, an yi mata tumbur bayan kashe saurayin da ta kwana da shi (Hotuna). Hoto daga Godwin George
Source: Facebook

KU KARANTA: Hotunan auren bazawara mai shekaru 50 da bazawari mai shekaru 60 sun kayatar

'Yar asalin Udi ce, kuma tana zama ne a jihar Enugu kafin a tura ta bautar kasa, kamar yadda ta wallafa a shafinta na Facebook.

Ta fara sanya kayan bautar kasa ne a ranar 17 ga watan Disamba, har ta wallafa hotuna 17 da kayan a shafinta na Facebook.

Kakakin NYSC na Akwa Ibom, Linus Edor, ya ce ba zai iya cewa komai ba tukunna, har sai ya tabbatar da Paschaline tana daya daga cikin masu bautar kasar.

A wani labari na daban, direbobin tifa a ranar Lahadi sun rufe babbar hanyar Gusau zuwa Sokoto bayan zargin kama mambobinsu da jami'an tsaro suke yi, TVC News ta wallafa hakan.

Wannan matakin da direbobin tifan suka dauka ya tsayar da motoci masu kaiwa da kawowa a Gada biyu na fiye da sa'o'i biyu a babbar hanyar.

Kungiyar na zargin jami'an NSCDC da cutar dasu matuka na kusan watanni shida.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel