Dokta Bashir: Idan mutum ya saki matarsa a shirin fim to ya saki matarsa ta gida ne

Dokta Bashir: Idan mutum ya saki matarsa a shirin fim to ya saki matarsa ta gida ne

- Shahararren malamin addinin Musulunci, Dr Bashir Aliyu ya yi karin haske kan batun sakin mata a wasan kwaikwayo

- Dr Bashir yace duk mutumin da ya furta saki ga matarsa a cikin shirin fim, toh lallai kuwa aure ya rabu tsakaninsa da matarsa ta gaske idan har yana da ita

- Ya ce wannan ita ce hakikanin fahimtarsa a kan hukuncin da koyarwar addinin musulunci ta tanadar game da sakin matar aure

Rahotanni sun kawo cewa Dr Bashir Aliyu, babban limamin masallacin Al-Furqan da ke Kano, ya yi wa’azin cewa duk wani dan wasan kwaikwayo da ya furta saki ga matarsa a cikin shirin fim, toh lallai kuwa aure ya rabu tsakaninsa da matarsa ta gaske idan har yana da ita.

Mallam Bashir ya bayyana matsayarsa ne a yayinda yake zantawa da manema labarai a wayar tarho, inda ya ce wannan ita ce ainahin fahimtarsa a kan hukuncin da koyarwar addinin Islama ta tanadar a kan sakin matar aure, jaridar Aminiya ta ruwaito.

A cewarsa, mas’ala ta fiqihun addinin musulunci ba kowa ne ke fassara a kanta ba, sai dai fassara da kuma bayyana fahimta a kan kowace mas’ala ta kebanta ne kadai ga malamai masu ilimin addinin.

Dokta Bashir: Idan mutum ya saki matarsa a shirin fim to ya saki matarsa ta gida ne
Dokta Bashir: Idan mutum ya saki matarsa a shirin fim to ya saki matarsa ta gida ne Hoto: @aminiyatrust
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Rikicin PDP ya munana yayinda kwamishinan Ikpeazu ya caccaki gwamnan da wasu bayan ya karbi bakuncin Orji Kalu

A wani faifan bidiyo da ke yawo a shafukan zumunta, an gano malamin yayinda yake bayar da fatawar cewa ko kadan babu wasa a masa’ala ta aure da saki a cikin addinin Musulunci.

Wannan fatawa ta malamin ya haddasa cece-kuce musamman a tsakanin masu amfani da zaurukan sada zumunta, inda da dama suka nuna adawa a kai.

Har ila yau, malamin ya sake fitar da wani bidiyon inda ya yi karin haske a kan fatawar da yayi kuma ya yi mata lakabi da “cikakken bayani a kan hukuncin wanda ya saki matarsa da wasa.”

“Wannan bayani ne wanda nake fitar da shi ga jama’ar Musulmi a kan abunda ya yadu a kafofin sada zumunta dangane da sha’anin saki da kuma abunda ya danganci ambatonsa a cikin wasan kwaikwayo. Wannan magana wanda yake a cikin darasi na tafsirin al-Qur’ani wanda nake yi a masallaci Al-Furqan ta sanya rudani a cikin fahimtar mutane wanda ya wajaba nayi bayani saboda na saita fahimta a cikin abunda yake shine na ambata.

“Na farko dai maganar nan ta zo ne a kan gaba ta bayanin tafsirin ayar Al-Qur’ani ta suratun Tauba da Allah Ta’alla yake cewa Ka ce musu ya, Da Allah ne da ayoyinsa da Manzonsa kuka kasance kuna yi wa Izgili, to a kan haka ne na yi bayanin cewa izgili da wargi da wasa idan ya danganci janibin Allah da Al-Qur’ani da Manzon Allah SAW yana da hadari, domin zai fitar da mutum daga addini.

Malamin ya kuma yi bayanin cewa izgilanci a kan lamarin da ya shafi hukunce-hukuncen shari'a shima yana da wani babi da yake hatsari, wanda a cewarsa shine lamari da ya danganci sakin aure da kuma komensa.

Ya ce saboda Manzon Allah S.A.W yana cewa, "abu uku gaskensu gaske ne, kuma warginsu ma gaske ne wato saki, aure da kome.”

“To a kan haka ne, na ce idan mutum ya furta saki ga matarsa ta aure a cikin wasan kwaikwayo, idan yana da matan a gaske, to wannan saki ya afku a kansu, sai dai maganar a dunkule take haka amma tana da fashin baki.

“Idan mutum a cikin wasan kwaikwayo ya kalli matarsa ta wasan kwaikwayo, ya ce, ke kin saku, ko ke wance na sake ki, to za a duba a gani, idan wannan matar wadda take cikin wasan kwaikwayon matarsa ce ta hakika tun kafin su yi wasan kwaikwayo ya zamanto da ita da shi duk suna shiri ne a cikin wasan kwaikwayon, to idan ya kalleta ya ce ya sake ta, duk da yake wasa ne, to wannan saki ya afku saboda wannan nassi na Hadisin Annabi S.A.W.

“Amma idan wannan mata wacce ke cikin wasan kwaikwayo ba matarsa ce ta aure ba, fim ne ko wasan kwaikwayo ne ya mayar da ita matarsa, to wannan saki bai samu mahalli ba, saboda haka matarsa ta aure babu abin da ya samu aurensa da ita.

“Idan kuma ya zo yana bayar da labari ne a cikin shirin fim din, misali aka ce yana bayar da labari a wata fitowa a cikin shirin wanda ya zamana yana bawa abokanansa labari cewa, to ai ni matana ma gaba ki daya sun saku, ko ya ce, ai ni matata ma na sake ta, to wannan maganar da ya yi, matarsa ta aure duk da yake ba ita yake nufi ba, idan har yana da matar ta aure, to wannan saki ya afku a kanta, saboda wannan hadisi na Manzon Allah kuma saboda ayar Al-Qur’ani wadda Allah yake cewa, kada ku dauki ayoyin Allah su zama abin wasa kuma wannan ayar ta sauka ne a kan saki.

KU KARANTA KUMA: Korona: Dalilin da yasa yan Nigeria da dama basu yarda akwai cutar ba

Sai dai ya ce malamai mabiya mazhabar Malik sun ce idan akwai wata shaida da ke nuna wasa yake yi, to wannan shaidar za ta taimaka masa ta nuna kan cewa sakin bai afku a kansa ba.

Ga cikakken bidiyon a kasa:

A wani labari na daban, rundunar ‘yan sanda reshen jihar Oyo ta tabbatar da kame wasu Fulani 47 dauke da makamai a yankin Igangan da ke karamar hukumar Ibarapa ta Arewa a jihar, The Sun ta ruwaito.

Jami'an tsaro na hadin guiwa na rundunar yaki da masu aikata laifuka ta jihar karkashin jagorancin sojoji ne suka damke mutanen dauke da makamai a kogin Ofiki da ke kan titin Tapa-Igangan.

An kama su ne bayan wasu sa’o’i bayan da Hukumar Tsaro ta Jihar Oyo, wanda aka fi sani da Amotekun Corps, ta kai samame a maboyar wasu da ake zargin masu satar mutane ne da safiyar Asabar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel