Rikicin PDP ya munana yayinda kwamishinan Ikpeazu ya caccaki gwamnan da wasu bayan ya karbi bakuncin Orji Kalu

Rikicin PDP ya munana yayinda kwamishinan Ikpeazu ya caccaki gwamnan da wasu bayan ya karbi bakuncin Orji Kalu

- Karban bakuncin sanata Orji Kalu da wani kwamishinan Gwamna Ikpeazu yayi na ci gaba da janyo cece-kuce

- Kwamishinan, Cosmos Ndukwe ya karbi bakuncin Kalu wanda ya kasance jigon APC a mahaifarsa da ke Abia

- Sai dai Ndukwe ya bayyana cewa bai aikata kowani laifi ba don ya tarbi jigon na jam’iyyar adawa a jihar

Guguwar sauyin sheka da tayi wa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) tsinke a yankin kudu maso gabas na iya ziyartan jihar Abia kwanan nan yayinda wasu jiga-jigan jam’iyyar suka fara tadi da shugabannin All Progressives Congress (APC) a yankin.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa kwamishinan kasuwanni da zuba jari na jihar Abia, Cosmos Ndukwe ya bayyana cewa gwamnan jihar, Okezie Ikpeazu da jam’iyyarsa ta PDP basa binsa bashi don ya karbi bakuncin Sanata Kalu a mahaifarsa.

KU KARANTA KUMA: Korona: Dalilin da yasa yan Nigeria da dama basu yarda akwai cutar ba

Rikicin PDP ya munana yayinda kwamishinan Ikpeazu ya caccaki gwamnan da wasu bayan ya karbi bakuncin Orji Kalu
Rikicin PDP ya munana yayinda kwamishinan Ikpeazu ya caccaki gwamnan da wasu bayan ya karbi bakuncin Orji Kalu Hoto: @GovernorIkpeazu
Asali: Twitter

Legit.ng ta tattaro cewa Ndukwe ya bayyana hakan bayan rigima da cece-kucce da ya barke kan ziyarar da sanatan mai wakiltan Abia ta arewa, Kalu ya kai masa a mahaifarsa ta Akanu Item.

An rahoto cewa kwamishinan yace ziyarar ta ta’aziyya ce sabanin rade-radin cewa ta siyasa ce.

Mataimakin Shugaban karamar hukumar Bande ta jihar, Promise Uzoma Okoro na daga cikin wadanda suka soki kwamishinan.

Ya ce Ndukwe makiri ne tunda ya caccaki kakakin majalisar dokokin Abia, Chinedum Orji kan ziyartan sanatan jam’iyyar mai adawa a baya.

Rahoton ya nuna cewa duk da kiraye-kirayen da ake masa na ba kakakin da sauransu hakuri a kan gagarumin sukar da yayi masa a baya, kwamishinan ya ce babu wanda yake binsa bashi ciki harda gwamnan jihar, Okezie Ikpeazu da jam’iyyarsa ta PDP.

A cewar jaridar, wata majiya kan lamarin ta ce Ndukwe ya bugi kirji a wani taron abokai da yan siyasa a kwanaki cewa babu abunda wani daga cikin wadanda ake magana a kai za su iya yi.

KU KARANTA KUMA: Dukkanku dajin Sambisa za ku garzaya, Buratai ga sojin da ake horarwa

Ya ce babu wanda ke binsa bashin ban hakuri kan abunda yayi.

A wani labarin, tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ya na kiran a samu hadin gambizar ‘yan siyasa da za su ceto kasar nan daga halin da ta samu kanta.

Jaridar Punch ta rahoto Sanata Rochas Okorocha yana wannan kira a lokacin da ya kaddamar da sabon titin Rumuche/Rumuakunde/Ohna Awuse a jihar Ribas.

A ranar Litinin, 11 ga watan Junairu, 2020, Sanatan na yammacin jihar Imo ya ziyarci Ribas, ya bude sabuwar hanyar da gwamna Nyesom Wike ya yi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel