Korona: Dalilin da yasa yan Nigeria da dama basu yarda akwai cutar ba

Korona: Dalilin da yasa yan Nigeria da dama basu yarda akwai cutar ba

Ba sabon labari bane cewa wasu yan Najeriya basu yarda da wanzuwar annobar korona ba. A ganinsu, mutane basa yanke jiki suna mutuwa a unguwanni kuma ba a samu abokai, abokan aiki da yan uwansu dauke da cutar ba.

A wannan rahoton, Legit.ng ta duba dalilan da suka sa yan Najeriya da dama basu yarda akwai cutar ba.

1. Yadda gwamnatin tarayya ke abubuwanta.

Duk da sakon da gwamnatin tarayya ke aikawa na cewa korona gaskiya ce, bata tabuka wani abun kirki don samun yardar yan Najeriya ba.

Gwamnatin na nuna yanayi biyu ta hanyar yin zabe a takunkuminta. Misali, ta bari an gudanar da wasu zauka.

Korona: Dalilin da yasa yan Nigeria da dama basu yarda akwai cutar ba
Korona: Dalilin da yasa yan Nigeria da dama basu yarda akwai cutar ba Hoto: @NCDCgov
Asali: Twitter

A kwanan nan ta umurci yan Najeriya da su yi lambobin yan kasa, duk da cewar ana tsaka da zagaye na biyu na wannan mugunyar annobar.

Hakazalika, gwamnati ta ki haramta wa jirage daga kasashen Birtaniya, Amurka da Afrika ta kudu inda annobar ta fi kamari shigowa kasar.

Dukka wadannan na sanya wa yan Najeriya kokwanto game da wanzuwar cutar. Mutane na ganin da ace akwai cutar da gaske, da gwamnati ba za ta bari ayi wadannan harkoki ba duba ga cewar taron jama’a zai yada abun, jaridar Punch ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Okorocha: Najeriya na bukatar ‘Yan siyasan kirki su hada-kai da nufin kawo gyara

2. Yadda wasu jami’an gwamnati, shugabannin siyasa, masu fada aji da shahararru ke abubuwa

Manyan mutane irin jami’an gwamnati, shugabannin siyasa, masu fada aji da shahararru basu taimaka ko kadan a kan halin da ake ciki.

A koda yaushe suna a wajen taro ba tare da bin ka’idar barin tazara a tsakani ba ko kuma sanya takunkumin fuska ba.

Wasu da dama suna shirya taro ko halartan bukukuwa, jana’iza, bukukuwan nnadin sarauta da sauransu.

Wadannan abubuwa na taimakawa wajen rura wutar rade-radin cewa annobar korona ba gaskiya bace.

3. Dabi’ar shugaannin addini game da cutar

Wasu rukunin mutane da rura wutar cewa cutar ba gaskiya bace sune wasu shugabannin addini wadanda suka karyata wanzuwar korona.

Da yadda suke abubuwa, suna dilmiyar da miliyoyin yan Najeriya da ke binsu.

KU KARANTA KUMA: Rahama Sadau na fuskantar caccaka sakamakon hoton da ta saki a yanar gizo

4. Dabi’ar wasu makirai

Yan Najeriya da dama suna karyata wanzuwar korona saboda wadannan mutane. Mutane masu dabi’ar shirya makirci kan tsara bayanai na bata da gangan da wasu bidiyo da kan yi fice sosai.

Harma wani faston Najeriya ya shiga cikin masu hada wannan makirci na karya, inda wasu mutane suka yarda da abun.

A wani labarin, hukumar NCDC mai yaki da yaduwar cututtuka a Najeriya ta ce Najeriya ta kai wani mataki mai kamari a yaki da ta ke yi da annobar Coronavirus.

Legit.ng ta samu labarin Darekta Janar na hukumar NCDC na kasa, Dr. Chikwe Ihekweazu ya na cewa asibitoci za su gagara sanin yadda za su yi da masu cutar.

Dr. Chikwe Ihekweazu ya bayyana haka ne a wasu bayanai da ya yi a shafinsa na Twitter a ranar Litinin.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel