Fitaccen dan siyasar Kano, Bello Isah Bayero ya mutu

Fitaccen dan siyasar Kano, Bello Isah Bayero ya mutu

- Jihar Kano ta rasa daya daga cikin manyan dattijan ta Alhaji Bello Isah Bayero daren Alhamis bayan gajeriyar jinya

- Marigayin ya rasu ya na da shekara 87 kuma dan uwa ne ga Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero

- Gwamna Ganduje ya aike da sakon ta'aziyya ga masauratar Kano tare da bayyana Bello a matsayin mutumin kirki

Wani babban dan siyasa a Kano, na hannu damar Shugaba Buhari kuma dan uwan Sarkin Kano, Alhaji Bello Isa Bayero, ya rasu, rahoton Daily Trust.

A cewar iyalan sa, ya rasu daren Alhamis yana da shekaru 87 a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano (AKTH) bayan yan gajeriyar jinya.

Fitaccen dan siyasar Kano, Bello Isah Bayero ya mutu
Fitaccen dan siyasar Kano, Bello Isah Bayero ya mutu. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Hanan Buhari tare da mijinta Turad sun tafi Dubai don bikin zagayowar ranar haihuwarsa (Bidiyo da Hotuna)

Shine jagoraran magoya bayan jamiyyar APC sannan ya taba rike shugaban hukumar aikin Hajji na kasa (NAHCON).

An haifi Bello a gidan sarautar Kano;kuma mahaifin sa kanin marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero ne.

Dan siyasa ne da ya da ya rike mukumai da dama a bangarorin gwamnati da na kashin kai.

Marigayin ya nemi takarar kujerar sanatan Kano ta tsakiya a majalisar dokoki sau da dama.

Tuni gwamna Ganduje ya aike da sakon ta'aziyya ga masauratar Kano bisa rashin dattijon.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa Sanata Adebayo Salami rasuwa

A wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan Abba Anwar ya fitar, gwamnan ya ce "mun samu labari cikin kaduwa, rasuwar Bello Isah Bayero, wanda ya rasu lokacin da jihar da kasa ke matukar bukatar sa.

"Mutumin kirki ne kwarai da gaske, wanda jagorancin sa ya taimaka wajen dawo da martabar damokradiyya".

A wani labarin daban, rikici ya kaure a zauren majalisar Jihar kasar Ghana a jiya Laraba 6 ga watan Janairu bayan rushe majalisar kunshi ta bakwai.

A cikin hoton bidiyon da ya karade shafukan dandalin sada zumunta, an gano rikici ne ya kaure tsakanin yan jam'iyyar NPP da NDC kan wacce jam'iyya ne ke da rinjaye kuma wacce zata fitar da sabon Kakakin Majalisa.

Kamar yadda bidiyon ya nuna, wasu daga cikin yan majalisar sun rika kai wa juna hannu sannan wasu suka rika fatali da akwatunan kada kuri'a da ke zauren majalisar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel