'Yan majalisar Ghana sun bawa hammata iska kan batun rinjaye (Bidiyo)
- Rikici ya barke a zauren majalisar kasar Ghana tsakanin yan jam'iyyar NPP da NDC
- 'Yan majalisar sun kacame da dambe kan jayayyar jam'iyyar da ke da rinjaye
- Daga bisani an tura jami'an sojoji zuwa zauren majalisar don tabbatar da doka da oda
Rikici ya kaure a zauren majalisar Jihar kasar Ghana a jiya Laraba 6 ga watan Janairu bayan rushe majalisar kunshi ta bakwai.
A cikin hoton bidiyon da ya karade shafukan dandalin sada zumunta, an gano rikici ne ya kaure tsakanin yan jam'iyyar NPP da NDC kan wacce jam'iyya ne ke da rinjaye kuma wacce zata fitar da sabon Kakakin Majalisa.
Kamar yadda bidiyon ya nuna, wasu daga cikin yan majalisar sun rika kai wa juna hannu sannan wasu suka rika fatali da akwatunan kada kuri'a da ke zauren majalisar.
DUBA WANNAN: Zaben kananan hukumomi: 'Yan takara 6 sun fadi gwajin miyagun kwayoyi a Kano
Rahotanni sun nuna cewa jam'iyyar NPP ce ke da rinjaye da kujeru 137 yayin da NDC ita kuma ke da kujeru 136.
Daga bisani dai an turo jami'an sojoji zuwa zauran majalisar domin dawo da doka da oda a zauren majalisar.
Ga hoton bidiyon nan a kasa;
KU KARANTA: Amsar Rahama Sadau game da batun dena fim bayan aure
A wani labarin daban, Sanata Elisha Abbo mai wakiltar mazabar Adamawa Ta Arewa a Majalisa ta 9 ya tabbatar da cewa zai yi takarar gwamna a Jihar Adamawa a shekarar 2023, The Punch ta ruwaito.
Abbo wanda ya bayyana hakan a Ganye kuma ya ce ya fice daga jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ne saboda jam'iyyar ta mutu.
A wurin gasar gano zakarun 'yan kwallon kafa da sashin matasa na kungiyar yakin neman zabensa ta shirya, mai suna Sanata Ishaku Abbo Ambassadors, (SIA Ambassadors), Abbo ya ce zai yi takarar kujerar gwamna a Adamawa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng