Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa Sanata Adebayo Salami rasuwa
- Allah ya yi wa jigo a jam'iyyar APC, Sanata Adebayo Salami rasuwa
- Tsohon dan takarar gwamnan a Osun ya rasu ne a daren ranar Alhamis a Amurka
- Babban dansa mai suna Oluwatoyin Salami ya tabbatar da rasuwar mahaifinsa
Tsohon dan majalisar dattawa kuma jigo a jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai wakiltar Jihar Osun , Senata Adebayo Salami ya riga mu gidan gaskiya, Independent ta ruwaito.
Salami, sanata a jamhuriya ta hudu da ya wakilci mazabar Osun Ta Tsakiya ya rasu ne a kasar Amurka a daren ranar Alhamis.
Ba a san takamammen abinda ya yi ajalinsa ba a lokacin hada wannan rahoton.
DUBA WANNAN: Za a yi jarrabawar 'kimiyyar shanu' ta kasar a India
Wasu rahotanni da ba a tabbatar da sahihancinsu ba sun ce akwai yiwuwar mutuwarsa na da alaka da annobar coronavirus.
An zabi Salami a matsayin sanata ne mai wakiltar Osun a shekarar 1999 a karkashin jam'iyyar Alliance for Democracy (AD) kuma ya yi rantsuwar fara aiki a ranar 29 ga watan Mayun shekarar ta 1999.
Dansa na farko, Oluwatoyin Salami ya tabbatar da rasuwar mahaifinsa yana da shekaru 68 a duniya.
KU KARANTA: NIN: Ma'aikatan NIMC sun fara yajin aiki saboda fargabar korona
An nada shi mamba a kwamitocin Kwadago, Mataimakin Shugaban kwamitin Makamashi da Karafa da kuma Albarkatun ruwa.
Shine kuma dan takarar gwamna na jam'iyyar National Republican Convention a jihar Osun inda ya fafata da marigayi Sanata Adetunji Adeleke na Social Democratic Party (SDP).
A wani labarin daban, rikici ya kaure a zauren majalisar Jihar kasar Ghana a jiya Laraba 6 ga watan Janairu bayan rushe majalisar kunshi ta bakwai.
A cikin hoton bidiyon da ya karade shafukan dandalin sada zumunta, an gano rikici ne ya kaure tsakanin yan jam'iyyar NPP da NDC kan wacce jam'iyya ne ke da rinjaye kuma wacce zata fitar da sabon Kakakin Majalisa.
Kamar yadda bidiyon ya nuna, wasu daga cikin yan majalisar sun rika kai wa juna hannu sannan wasu suka rika fatali da akwatunan kada kuri'a da ke zauren majalisar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng