Hanan Buhari tare da mijinta Turad sun tafi Dubai don bikin zagayowar ranar haihuwarsa (Bidiyo da Hotuna)

Hanan Buhari tare da mijinta Turad sun tafi Dubai don bikin zagayowar ranar haihuwarsa (Bidiyo da Hotuna)

- Hanan Buhari, yar autar shugaban Najeriya, Muhammad Buhari ta taya mijinta Turad Sha'aban murnar zagayowar ranar haihuwarsa

- Hanan da Turad tare da wasu 'yan uwa da abokan arziki sun tafi birnin Dubai inda suka yi shagali tare da taya Turad murna

- An daura auren Hanan da mijinta Turad ne a watan Satumban shekarar 2020 a fadar shugaban kasa da ke Abuja

Diyar Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Hanan Buhari-Sha'aban ta taya mijinta, Muhammad Turad Sha'aban murnar zagayowar ranar haihuwarsa.

Ma'auratan sunyi tattaki zuwa Dubai da ke Hadadiyar Daular Larabawa, UAE, son shagalin zagayowar ranar haihuwar na Turad.

Hanan Buhari tare da mijinta Turad sun tafi Dubai don bikin zagayowar ranar haihuwarsa (Hotuna)
Hanan Buhari tare da mijinta Turad sun tafi Dubai don bikin zagayowar ranar haihuwarsa (Hotuna)
Source: Instagram

An daura auren Hanan da Turad ne a watan Satumban shekarar 2020. Turad ya kara shekara guda a duniya a ranar Alhamis.

DUBA WANNAN: NDLEA ta fitar da sunayen wadanda suka yi nasara da za a dauka aiki

Hanan ta wallafa hoton bidiyo a Instastory, a ranar 8 ga watan Janairu inda aka gano ma'auratan suna cin abinci tare da iyalai da abokai na kusa.

Ta yi wa bidiyon lakabi da;

"Ina taya ka murnar zagayowar ranar haihuwar ka @Mohd Turad"

Kazalika, yar uwar Turad, Fateema Ajimonlbi ita ma ta wallafa wasu hotuna da bidiyo na kwarya kwaryar liyafar cin abincin da suka shirya.

Ga bidiyo da hotunan a kasa;

Hanan Buhari tare da mijinta Turad sun tafi Dubai don bikin zagayowar ranar haihuwarsa (Hotuna)
Hanan Buhari tare da mijinta Turad sun tafi Dubai don bikin zagayowar ranar haihuwarsa (Hotuna)
Source: Instagram

Hanan Buhari tare da mijinta Turad sun tafi Dubai don bikin zagayowar ranar haihuwarsa (Hotuna)
Hanan Buhari tare da mijinta Turad sun tafi Dubai don bikin zagayowar ranar haihuwarsa (Hotuna)
Source: Instagram

Hanan Buhari tare da mijinta Turad sun tafi Dubai don bikin zagayowar ranar haihuwarsa (Hotuna)
Hanan Buhari tare da mijinta Turad sun tafi Dubai don bikin zagayowar ranar haihuwarsa (Hotuna)
Source: Instagram

A wani labarin daban, rikici ya kaure a zauren majalisar Jihar kasar Ghana a jiya Laraba 6 ga watan Janairu bayan rushe majalisar kunshi ta bakwai.

A cikin hoton bidiyon da ya karade shafukan dandalin sada zumunta, an gano rikici ne ya kaure tsakanin yan jam'iyyar NPP da NDC kan wacce jam'iyya ne ke da rinjaye kuma wacce zata fitar da sabon Kakakin Majalisa.

Kamar yadda bidiyon ya nuna, wasu daga cikin yan majalisar sun rika kai wa juna hannu sannan wasu suka rika fatali da akwatunan kada kuri'a da ke zauren majalisar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel