Trump ya samu mabiya 2.4 a sabon shafin na Parler Bayan dakatar da shi a Tuwita, Facebook, da Instagram

Trump ya samu mabiya 2.4 a sabon shafin na Parler Bayan dakatar da shi a Tuwita, Facebook, da Instagram

- Manhajojin Tuwita, Facebook, da Instagram, sun dakatar da shugaban kasar Amurka, Donald Trump, daga amfani da kafafensu

- Trump ya yi kaurin suna wajen amfani da dandalin sada zumuna dominn yada labaran kanzon kurege da ingiza masoya da magoya bayansa

- Yanzu haka Trump ya sake samun magoya baya miliyan 2.4 a cikin sa'a daya da bude sabon shafi a manhajar Parler

A ranar Alhamis ne shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya bude sabon shafi a manhajar Parler biyo bayan dakatar da shi a manhajar Tuwita, Facebook, da Instagram.

Manhajojin Tuwita, Facebook, da Instagram sun dakatar da Trump bisa zarginsa da amfani da kafafen wajen ingiza magoya bayansa.

Jarida TheCable ta rawaito cewa Trump ya samu mabiya miliyan 2.4 cikin sa'a daya da bude shafi a Parler.

KARANTA: Wata daban: Daliban BUK sun ce basu shirya komawa makaranta ba tukunna, sun bayyana dalilansu

Jagoran 'yan jam'iyyar Democrat a majalisar dattijan kasar Amurka, Chuck Schumer, ya yi kiran a gaggauta tsige Donald Trump saboda rikicin da magoya bayansa suka haddasa.

Trump ya samu mabiya 2.4 a sabon shafin na Parler Bayan dakatar da shi a Tuwita, Facebook, da Instagram
Trump ya samu mabiya 2.4 a sabon shafin na Parler Bayan dakatar da shi a Tuwita, Facebook, da Instagram Hoto: @Thecableng
Asali: Twitter

A wani jawabi da Schumer ya fitar ranar Alhamis, ya ce 'yan tawayen da suka kutsa cikin Capitol suna da daurin gindin Trump.

KARANTA: Ina kisa ne domin kawai na samu kudin shan giya da shagwaba budurwata - Matashi Tajudeen

"Wannan cin mutunci ne da zubar da kimar kasar Amurka, wanda kuma shugabanta ya jawo mata.

"Bai kamata shugaban kasa ya cigaba da zama ofis ba, bai kamata ya kara ko kwana daya a kan kujerarsa ba," a cewar Schumer.

Legit.ng Hausa ta rawaito cewa akalla sinadarai masu fashewa guda biyu aka gano a Washington DC sakamakon rikicin da ya barke a Amurka, kamar Premium Times ta samu rahotanni daga kasar.

Kazalika, jaridar Punch ta rawaito cewa majiyarta a kasar Amurka ta tabbatar mata da mutuwar wata mata da sanarwa ta bayyana cewa ta samu rauni sakamakon harbin bindiga.

Rikici ya barke a Capitol, Washington, bayan magoya bayan shugaba Trump sun yi kutse domin dakatar da tabbatar da nasarar Joe Biden.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel