An harbe wata mata, an gano sinadarai masu fashewa a rikicin da ya barke a Amurka
- Sabon rikici ya barke a kasar Amurka yayin da ake saka ran cewa za'a samu musayar ikon mulkin Amurka a karshen Janairu
- Rikici ya barke ne yayin da magoya bayan shugaba Trump suka kutsa cikin Capitol domin dakatar da tabbatar da nasarar Joe Biden
- Har yanzu shugaba Trump ya ki saduda, ya hakura, ya karbi kayen da ya sha a hannun Joe Biden, dan takarar jam'iyyar Democrat
A kalla sinadarai masu fashewa guda biyu aka gano a birnin Washington DC sakamakon rikicin da ya barke ranar Laraba, kamar yadda Premium Times ta samu rahotanni daga kasar Amurka.
Kazalika, jaridar Punch ta rawaito cewa majiyarta a kasar Amurka ta tabbatar mata da mutuwar wata mata da sanarwa ta bayyana cewa ta samu rauni sakamakon harbin bindiga.
Rikici ya barke a Capitol, Washington, bayan magoya bayan shugaba Trump sun yi kutse domin dakatar da tabbatar da nasarar da Joe Biden ya samu a zaben da aka yi a watan Nuwamba, 2020.
KARANTA: Ina kisa ne domin kawai na samu kudin shan giya da shagwaba budurwata - Matashi Tajudeen
Jaridar The New York Times ta rawaito cewa an gano bam na farko a hedikwatar kwamitin jam'iyyar Republican da ke Beltway.
Kazalika, rahoton jaridar ya bayyana cewa an samu wani kunshi mai cike da alamun tambaya a hedikwatar kwamitin jam'iyyar Democrat.
Premium Times ta rawaito kafar NBC na yin kari da cewa an sake samun wani sinadari mai fashewa a harabar Capitol da masu zanga-zanga suka yi wa tsinke.
KARANTA: Wata daban: Daliban BUK sun ce basu shirya komawa makaranta ba tukunna, sun bayyana dalilansu
Shugaba Trump ya bukaci magoya bayansa, da suka mamaye Capitol, su koma gida, tare da sanar da su cewa ya fahimci irin radadin da suke ji, amma duk da haka ya fi son zaman lafiyarsu.
A karshen watan Janairu ake sa ran Trump zai mika mulkin kasar Amurka ga Joe Biden duk da har yanzu ya kafe kan cewa shine ya lashe zabe kuma shi za'a sake rantsarwa a karo na biyu.
A nan gida Nigeria, Legit.ng Hausa ta rawaito cewa fadar shugaban kasa ta yi raddi tare da yi wa jam'iyyar adawa ta PDP kaca-kaca.
A wani jawabi da Garba Shehu, kakakin shugaban kasa, ya fitar, fadar shugaba kasa ta ce duk wani sauran tasiri da PDP keda shi ya kare saboda ta zama jami'ar karya, kamar yadda Daily Trust ta rawaito.
A cewar fafa shugaban kasa, jam'iyyar PDP ba ta yi komai ba a tsawon mulkinta na shekaru goma sha shidda bayan assasa cin hanci da rashawa.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng