Daliban BUK sun ce basu shirya komawa makaranta ba tukunna, sun bayyana dalilansu
- Kungiyar malaman jami'o'i (ASUU) ta janye yajin aiki da ta shafe watanni tara tana yi
- Tun bayan sanar da janye yajin aikin, Jami'o'i sun cigaba da sanar da ranakun da zasu bude makarantunsu
- Wasu daliban Jami'ar BUK sun bayyana cewa da sauran rina a kaba, su ma basu shirya komawa makaranta ba
Alamu na nuna cewa da yawa daga cikin ɗaliban jami'ar BUK ba za su koma karatu a ranar 18 ga Janairu ba kamar yadda hukumar gudanarwar jami'ar ta sanar, a cewar HumAngle.
Kwana ɗaya da sanarwar janye yafin aiki na tsawon wata tara da ƙungiyar malaman jami'o'in ƙasar nan ta yi, da yawan ɗaliban jami'o'i sun nuna rashin shirinsu na komawa makarantar a lokacin da aka sanar.
"Ban jima da samun gurbin karatu na digiri na biyu a bangare nazari kan sadarwa ba. Amma sam bana tsammanin dalibai sun shiryawa cigaba da karatu haka da wuri." In ji wani mai suna Al’ameen Usman Abubakar.
Abubakar ya cigaba da cewa; "Kamata ya yi ace hukumar gudanarwar ta kammala yin rijista kafin 18 ga Janairu."
KARANTA: Da gyara a jawabinka na sabuwar shekara; Dattijan arewa sun aika sako ga Buhari
Ya bukaci jami'ar da ta ƙara lokacin yin rijistar zuwa watan Fabrairu don ɗalibai su samu damar shiryawa kan lokaci.
Ya bukaci jami'ar da ta ƙara lokacin yin rijistar zuwa watan Fabrairu domin sauran ɗalibai su samu damar shiryawa kan lokaci.
Wani ɗalibi mai suna Aminu Muhammad na tsangayar nazarin zamantakewa (Sociology) ya bayyana dalilansa da cewa: "Lahadin da ta wuce ne ma na iya samun shiga shafin yanar gizo na makarantar domin yin rijista wanda har yanzu ake yi."
KARANTA: Kano: Rundunar 'yan sanda ta kamo aljani bayan wani mutum ya shigar da kararsa (bidiyo)
Ya cigaba da cewa "Na gama biyan duk wasu kuɗaɗe amma har yanzu ban samu gurbi a jami'ar ba."
Aminu ya yi ƙorafin cewa zai yi wahala ace shi ya samu damar kammala rijistarsa kafin 18 ga Janairu.
Hasiya Abubakar, ɗaliba mai nazarin biochemistry cewa ta yi, "Dawowa karatun nan ya zo mana babu tsammani duk ɗalibai sun gaji da zaman gida."
A wani labarin na Legit.ng, Nyesom Wike, gwamnan jihar Ribas, ya ce 'yan Nigeria sun kosa shekarar 2023 ta zo domin PDP ta koma mulkin kasa.
Gwamna Wike ya bukaci jam'iyyar APC ta yi koyi da abin da PDP ta yi a shekarar 2015 na mika mulki bayan faduwa zabe.
Wike ya gargadi jam'iyyar APC akan kar ta kuskura ta yi yunkurin sauya zabin 'yan Nigeria a shekarar 2023.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng