Ina kashe mutane ne domin kawai na samu kudin shan giya da shagwaba budurwata - Mai laifi
- Dubun wani matashi da abokansa da ke kashe mutane domin yn tsafi tare da sayar da sassan jikinsu ta cika
- Matashin, Tajudeen Monsuru, ya ce yana cin naman mutane tare da korawa da ruwan giya duk lokacin da ya yi nishadi
- Ya bayyana cewa suna yaudarar mutane ta hanyar yi musu kirki tare da sakin jiki da su kafin daga baya su kashesu
Wani mutum ɗan shekara 30 mai suna, Tajudeen Monsuru, ya amsa laifin da ake zarginsa na amfani da sassan jikin mutum yana yin tsafi tare cin naman yana korawa da ruwan giya duk lokacin da yake cikin nishaɗi.
Da ya ke amsa tambayoyin yan jarida lokacin da hukumar yan sanda ta yi holinsa shi da wasu masu laifin a hedkwatarsu dake Osogbo cikin jihar Osun, ya ce shi da budurwarsa ne da mai suna Alan Mutiyat.
"Muna kashe mutane ne bayan sun aminta da mu. Mafi yawan lokuta har bacci muke yi tare kafin cikin dare mu kashe su mu yi gunduwa-gunduwa da su don sayar da sassan jikinsu.
KARANTA: Adadin mutanen da kowacce jiha ta rasa sakamakon ayyukan ta'addanci a 2020
"Bayan na sayar sai kuma na tafi gun shakatawa da ake sayar da barasa.
"Na taba kashe budurwata da wani mutum da abokina, Akeem, ya kawo shi. Bana jin komai bayan na aikata kisa su," a cewarsa.
KARANTA: NIMC ta kirkiro manhajar katin dan kasa a kan wayoyin hannu
Abokin harkar tasa mai suna Hamzat Akeem ɗan shekara 25, ya amsa cewa shi ya kawo budurwarsa, Gafari, gun Monsuru, inda suka kashe ta aka bashi ₦5,000 saboda rawar da ya taka.
Shi kuma wani mai suna Awayewasere Yusuf mai shekara 37 ya sayi kan budurwar akan farashin ₦20,000 domin yin tsafin samun kuɗi.
A wani labarin na Legit.ng, wata budurwa ta ci amanar wani saurayinta da ya ci amanar matarsa ta hanyar gabatar da ita a matsayin matar abokinsa da za'a koyawa sana'ar dinki.
Bayan matar mutumin ta saki jiki da dadiron mijinta, ta ci amanarta, ta gudu da jaririyarta da kuma katinta na ATM da ta aiketa da shi.
Bayan ya shiga hannun 'yan sanda, mijin matar ya amsa cewa budurwar masoyiyarsa ce amma bashi da hannu a batun sace jaririyarsu.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng