Zaben kananan hukumomi: 'Yan takara 6 sun fadi gwajin miyagun kwayoyi a Kano

Zaben kananan hukumomi: 'Yan takara 6 sun fadi gwajin miyagun kwayoyi a Kano

Hukumar zabe ta jihar Kano KANSIEC tayi watsi da yan takara shida bayan sun gaza tsallake gwajin kwayoyi

- Prof Sheka, shugaban hukumar ya ce jamiyyun da yan takarar su ka fito na iya maye gurbin yan takarar cikin satin nan

- Wasu majiyoyi daga hukumar NDLEA sun bayyana cewa yan takara 20 ne shida kamar yadda KANSIEC tayi ikirari ba

Gabanin zaben 16 ga Janairu na kananan hukumomin jihar Kano, hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar (KANSIEC) a ranar Laraba ta ce tayi watsi da yan takara shida saboda sun kasa tsallake gwajin kwayoyi, Daily Trust ta ruwaito.

Daily Trust ta ruwaito KANSIEC ta ce da kirkiri gwajin kwayoyi kuma wajibi ne ga duk dan takarar da ke son neman kujerar shugaban karamar hukuma ko kansila a zabe me zuwa saboda yawaitar shaye shaye a jihar.

'Yan takara 6 sun fadi gwajin miyagun kwayoyi a Kano
'Yan takara 6 sun fadi gwajin miyagun kwayoyi a Kano. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun sace matar kansila da wasu mutane 3 a Abuja

Shugaban hukumar, Prof Garba Ibrahim Sheka, wanda ya tabbatar da batun yayin da yake zantawa da Daily Trust akan shirye shiryen da hukumar ke yi na zaben, ya ce sun gano yan kwaya shida daga cikin yan takarar.

Ya ce, "bayan gwajin kwayoyin da hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA ta gudanar ga duk yan takarar ciyamomi 44 da kansiloli 484, an tabbatar da shida daga ciki yan kwaya ne kuma mun cire su daga yan takara.

"Duk yan takarar shida kujerar kansila suke nema babu dan takarar ciyaman.

"Jamiyyun su na iya amfani da wannan satin don gabatar da wasu yan takarar", in ji Sheka.

KU KARANTA: Kanin mataimakin gwamnan Jihar Legas ya rasuwa bayan kamuwa da korona

Sheka ya bayyana cewa dokar zata zama izna ga matasa masu sha'awar siyasa da su guji shaye shaye.

Sai dai, wasu majiyoyi daga NDLEA sun bayyana cewa mutane 20 ne, ba shida kamar yadda KANSIEC tayi ikirari ba, aka tabbatar da yan kwaya ne kuma ciki har da yan jamiyyar APC mai mulkin jihar

A wani labari na daban, hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Jihar Kano (PCACC) ta bankado ayyukan almundahana a tallafin karatun kasashen waje na gwamnatin jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban hukumar, Magaji Rimingado, wanda ya bayyana haka ga yan jarida ranar Talata, ya ce daga 2015 zuwa 4 ga Janairun 2021, gwamnatin jihar ta kashe naira biliyan 7 a tsarin wanda ta gada daga gwamnatin da ta gabata, amma ana samun korafin daliban da suka rage a kasashen waje.

Ganin yadda korafe korafe suka yi yawa kuma ya kamata ace da yawa yawancin daliban sun kammala karatun su, gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje ya umarci hukumar da tayi "bibiya", bincika ta kuma dauki mataki akan badakalar", in ji Rimingado.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel