Hukumar yaki da rashawa ta Kano ta gano almundahana a hukumar bada tallafin karatu

Hukumar yaki da rashawa ta Kano ta gano almundahana a hukumar bada tallafin karatu

- PCACC ta bankado almundahanar da aka tafka a tallafin karatun kasashen waje da gwamnatin Kano ke daukar nauyi

- Shugaban hukumar, Barrister Muhuyi Rimingado ya ce har yanzu gwamnati na ci gaba da biyan kudade

- Ya kuma ce wasu mutanen ne suke son lalata tsarin da kuma matsawa gwamnati lamba

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Jihar Kano (PCACC) ta bankado ayyukan almundahana a tallafin karatun kasashen waje na gwamnatin jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban hukumar, Magaji Rimingado, wanda ya bayyana haka ga yan jarida ranar Talata, ya ce daga 2015 zuwa 4 ga Janairun 2021, gwamnatin jihar ta kashe naira biliyan 7 a tsarin wanda ta gada daga gwamnatin da ta gabata, amma ana samun korafin daliban da suka rage a kasashen waje.

Hukumar yaki da rashawa ta Kano ta gano almundahana a hukumar bada tallafin karatu
Hukumar yaki da rashawa ta Kano ta gano almundahana a hukumar bada tallafin karatu. @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Budurwa ta gaji da ganin mahaifiyarta babu miji, ta bazama nema mata a Twitter

Ganin yadda korafe korafe suka yi yawa kuma ya kamata ace da yawa yawancin daliban sun kammala karatun su, gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje ya umarci hukumar da tayi "bibiya", bincika ta kuma dauki mataki akan badakalar", in ji Rimingado.

Binciken farko, a cewar sa, ya nuna cewa adana bayanan tsarin ya zama abi mai matukar wahala saboda "tun da farko, ofishin sakataren gwamnatin jiha, ma'aikatar ilimi mai zurfi da kuma hukumar tallafin karatu ne suke gudanar da tsarin" sai kuma masu bada shawara a matsayin yan tsakiya wanda ya saukaka yadda za a iya lalata tsarin.

KU KARANTA: Akwai ƙyakyawar alaƙa tsakani na da Ganduje da Kwankwaso, in ji Shekarau

Ya ce wasu masu bada shawara da wasu "tsirarun yan siyasa" su ka zama masu bada rahotonnin karya kan tallafin tare da yunkurin kawo nakasu a tsarin, tare da matsawa gwamnati lamba.

Daga cikin ayyukan zambar da aka gano a binciken farko akwai shigar da sunan daliban da suka kammala karatu don gwamnati ta dinga biyan su.

Ya ce hukumar ba zata boye komai a binciken ba amma ya na da muhimmanci al'umma su sani har yanzu gwamnati ta na ci gaba da biyan kudaden tallafin.

Daily Trust ta ruwaito cewa, tsarin an fara shi ne zamanin mulkin Rabiu Musa Kwankwaso, ya zama abin cecekuce, da zarge zarge tun daga waccan gwamnati har zuwa wannan kan halin da daliban ke ciki a kasar waje, inda da yawa daga cikin daliban ke ikirarin gwamnati ta yi watsi da su.

A wani labarin, gwamna Babagana Zulum na jihar Borno a ranar Litinin ya aza harsashin gina jami'ar Al-Ansar, jami'a ta farko mai zaman kanta a jihar.

Zulum wanda gwamnatin sa ta bada fili mai girman hekta 100 ga gidauniyar Al-Ansar don gina jami'ar, ya kuma umarci da a gina titi mai nisan kilo mita 2.3 da kuma bohol a jawabin da ya gabatar wajen taron.

Zulum ya kuma umarci ma'aikatar ilimi mai zurfi da su bibiyi wanda ya samar da jami'ar don ganin yadda gwamnati zata iya ci gaba da tallafawa aikin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel