Kanin mataimakin gwamnan Jihar Legas ya rasuwa bayan kamuwa da korona

Kanin mataimakin gwamnan Jihar Legas ya rasuwa bayan kamuwa da korona

- Allah ya yi wa, Dakta Haroun Hamzat, kanin mataimakin gwamnan Jihar Legas, Obafemi Hamzat rasuwa

- Dakta Haroun ya rasu ne sakamakon kamuwa da cutar covid 19 da aka fi sani da coronavirus

- Kafin rasuwarsa, Dakta Haroun Hamzat ya yi aiki a hukumar lafiya bai daya da ke karamar hukumar Orile ta Jihar Legas

Obafemi Hamzat, mataimakin gwamnan Jihar Legas ya rasa kaninsa, Haroun, sakamakon kamuwa da cutar coronavirus da ya yi, The Cable ta ruwaito.

Kafin rasuwarsa, yana aiki ne a cibiyar lafiya bai daya da ke Karamar Hukumar Orile Agege da ke Jihar.

Kanin mataimakin gwamnan Jihar Legas ya rasuwa bayan kamuwa da korona
Kanin mataimakin gwamnan Jihar Legas ya rasuwa bayan kamuwa da korona. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Bidiyon Sarkin Bauchi yana waƙar kiristoci tare da 'matan zumunta' ya janyo cece-kuce

A cikin wata sanarwa da ta fitar, Kungiyar Likitocin Najeriya, NMA, reshen Jihar Legas ta ce tana cikin alhani bisa rasuwarsa.

"Muna sanar da rasuwar abokin aikin mu, Dakta Haroun Hamzat, wanda ya rasu yana da shekaru 37 a duniya," in ji sanarwar.

"Ya yi aiki a matsayin jami'in lafiya a daya daga cikin cibiyoyiin lafiya bai daya a karkashin karamar hukumar Orile kafin rasuwarsa.

KU KARANTA: 'Yan ta'adda sun kai hari Monguno

"Muna taya iyalansa, abokansa, abokan aiki da ma'aikatan PHC ta jihar Legas. Muna adduar Allah ya kiyaye 'yan uwanmu daga irin wannan mutuwar ta masu karancin shekaru.

"Muna adduar Allah ya bawa iyalansa da dukkan mu hakurin jure rashinsa. Amen. Muna bankwana da dan uwan mu likita, Dakta Haroun Hamzat. Allah ya jikanka da rahama. Amin."

A halin yanzu Najeriya na fuskantar annobar korona karo na biyu.

A wani labari na daban, hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Jihar Kano (PCACC) ta bankado ayyukan almundahana a tallafin karatun kasashen waje na gwamnatin jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban hukumar, Magaji Rimingado, wanda ya bayyana haka ga yan jarida ranar Talata, ya ce daga 2015 zuwa 4 ga Janairun 2021, gwamnatin jihar ta kashe naira biliyan 7 a tsarin wanda ta gada daga gwamnatin da ta gabata, amma ana samun korafin daliban da suka rage a kasashen waje.

Ganin yadda korafe korafe suka yi yawa kuma ya kamata ace da yawa yawancin daliban sun kammala karatun su, gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje ya umarci hukumar da tayi "bibiya", bincika ta kuma dauki mataki akan badakalar", in ji Rimingado.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164