'Yan bindiga sun sace matar kansila da wasu mutane 3 a Abuja

'Yan bindiga sun sace matar kansila da wasu mutane 3 a Abuja

- Yan bindiga sun yi garkuwa da iyalan kansila mai wakiltar mazabar Gwako da ke Gwagwalada a Abuja

- Yan bindigar sun bukaci kudin fansar da ya kai naira miliyan 200 tun da fari sai dai sunyi ragi bayan tsananta roko

- Ba a samu sukunin jin ta bakin rundunar yan sanda ba dangane da faruwar al'amarin

Masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da matan Idris Mohammed, kansila mai wakiltar mazabar Gwako da ke Gwagwalada, guda biyu hade da karin wasu mutane uku a birnin tarayya Abuja.

Ba a bayyane sunan matan kansilam su biyu ba, kanwar sa mace da kuma kannen sa maza su biyu ba har yanzu.

Wani makwabci, wanda ya nemi a sakaya sunan shi, ya ce lamarin ya faru da misalin 12:08 na daren Litinin, lokacin da yan bindiga dauke da makamai suka yi wa gidan kansilan kawanya a kauyen.

Yan bindiga sun sace matar kansila da wasu mutum 3 a Abuja
Yan bindiga sun sace matar kansila da wasu mutum 3 a Abuja. Hoto: @daily_trust
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Bidiyon Sarkin Bauchi yana waƙar kiristoci tare da 'matan zumunta' ya janyo cece-kuce

Ya ce yan bindigar sun lalata babbar kofar shiga gidan bayan sun ragargaza ta da harsashi.

Daga nan, sai suka kutsa gidan suka kuma kwashe matan sa da kanwar sa da kuma kannen sa biyu lokacin barin wutar.

Ya ce kansilan, wanda yake dakin sa, ya sha da kyar ta wata kofar fita bayan ya gane cewa masu garkuwa da mutane ne suka kawo hari.

"Sai lokacin da ya fuskanci cewa maharan masu garkuwa da mutane ne, sai ya nemi tsira ta kofar baya.

"Yanzu sun yi gaba da matan shi biyu, kanwar sa da kuma kannen maza da suke tare da shi," a cewar sa.

KU KARANTA: Anyi garkuwa da mutum 20, an kashe mutum daya a Nasarawa

Ya shaida cewa iyalan su sun sami sukunin tattaunawa da yan bindigar ranar Talata, kuma sun bukaci miliyan dari biyu kudin fansa.

"Amma maganar da nake yi yanzu sun rage kudin zuwa miliyan dari.

Amma bayan tsananta roko sun dawo da kudin miliyan sha biyar," in ji shi.

Ya kara da cewa daya daga cikin matan kansilan na da tsohon ciki.

Har yanzu ba a samu jin ta bakin mai magana da yawun rundunar yan sandan birnin tarayya Abuja, ASP Maryam Yusuf ba, bata daga waya ko tayi martanin sakon da aka tura mata ba.

A wani labari na daban, hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Jihar Kano (PCACC) ta bankado ayyukan almundahana a tallafin karatun kasashen waje na gwamnatin jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban hukumar, Magaji Rimingado, wanda ya bayyana haka ga yan jarida ranar Talata, ya ce daga 2015 zuwa 4 ga Janairun 2021, gwamnatin jihar ta kashe naira biliyan 7 a tsarin wanda ta gada daga gwamnatin da ta gabata, amma ana samun korafin daliban da suka rage a kasashen waje.

Ganin yadda korafe korafe suka yi yawa kuma ya kamata ace da yawa yawancin daliban sun kammala karatun su, gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje ya umarci hukumar da tayi "bibiya", bincika ta kuma dauki mataki akan badakalar", in ji Rimingado.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel