Haɗari ne gabatar da allurar rigakafin COVID-19 a Najeriya yanzu - Masanan Kwayar Cuta

Haɗari ne gabatar da allurar rigakafin COVID-19 a Najeriya yanzu - Masanan Kwayar Cuta

- Masana a Cibiyar Nazarin Likitocin Najeriya sun siffanta rigakafin Korona da hadari ga 'yan Najeriya

- Masanan sun ba da bayanin cewa, ba a san yanayin dadewar rigakafin a jiki ba

- Masanan sun shawarci gwamnati ta dakata sai an samo wasu bayanai a kan rigakafin

Masana ilimin Kawayar Cuta sun shawarci Gwamnatin Tarayya game da sayen maganin rigakafin COVID-19 a wannan lokacin, suna masu cewa ba shi da bukatar gabatar da shi yanzu ga ‘yan Najeriya.

Wata masaniyar kwayar cutar a Cibiyar Nazarin Likitocin Najeriya, Farfesa Rosemary Audu, a wata hira da ta yi da wakilin jaridar The Punch, ta ce ba za a bukaci allurar rigakafin ba idan kashi 70 cikin 100 na al’ummar kasar nan sun samar da kwayoyin kariya daga kwayar.

KU KARANTA: Gwamnatin Tarayya za ta raba wa mata 125,000 tallafin kudi N20,000 - Ministar Jin Kai

Haɗari a gabatar da allurar rigakafin COVID-19 a Najeriya yanzu - Masanan Kwayar Cuta
Haɗari a gabatar da allurar rigakafin COVID-19 a Najeriya yanzu - Masanan Kwayar Cuta Credit: BBC World News
Asali: Facebook

Ta ce, “Mun san cewa mutane da yawa sun kamu da cutar; zamu so sanin ko muna da garken kwayoyin kariya. Shin mutane suna da kwayoyin? Shin suna da rigakafin kariya tuni? Wani kashi na yawan jama'a ke da kwayoyin kariyar?

"Idan muna da kusan kashi 70 cikin 100 na yawan jama'ar da suka samar da kwayoyin kariya game da kwayar, cutar to za mu iya cewa muna da garken kwayoyin kariya kuma ba lallai ne mu bukaci allurar ba. Wannan wani abu ne wanda na tabbata a cikin yan watanni masu zuwa ya kamata mu iya fada.

“NIMR na gudanar da bincike kan ilimin cututtuka inda muke bincika ‘yan ƙasa game da matakan kwayar kariyar su da wannan kwayar cutar. Na tabbata nan ba da jimawa ba, za mu iya bayar da shawarar ko alluran za su amfane mu ko a'a."

Daraktan, Kimiyyar Kwayar Cutar Dan Adam da Dabbobi, na Kwalejin Kimiyya ta Jami'ar Legas, Farfesa Sunday Omilabu, a wata hira da wakilin The Punch ya ce zai zama da hadari gabatar da rigakafin COVID-19 ga ’yan Najeriya a wannan lokacin.

Ya ce, “Akwai wani abu a cikinmu wanda ke rage karfin kwayar cutar a jikinmu. Za mu iya kiranshi wani nau'in rigakafi da muke jin daɗi ta yanayinmu. Wannan yana zuwa mana a matsayin fa'ida; muna da wannan garkuwar a yanzu, idan wani abu ya shigo yanzu, zai iya lalata abin da muke amfana da shi a jikinmu.

KU KARANTA: Abubuwa masu rikitarwa a kasafin kudin 2021

“A gare mu, zan ba da shawarar cewa su ba mutane damar yin amfani da garken kwayoyin kariyarsu wanda suke morewa kuma kyauta ce ta dabi'a. Yakamata su maida hankali kan waɗancan mutane kadan din da ke da wasu larurar lafiya wanda ya sanya matakin garkuwar garkensu ya yi rauni sosai. Alurar rigakafin tana da haɗari yanzu saboda ba mu san yadda za ta daɗe ba.”

A wani labarin daban, Wani asibiti a Warsaw yana cikin tashin hankali saboda yin allurar rigakafin COVID-19 ga mashahurai da 'yan siyasa, wanda ya haifar da fushin jama'a kuma ya haifar da binciken gwamnati wanda ya fara a ranar Litinin, jaridar The Punch ta ruwaito.

Poland, wacce kamar yawancin kasashen Turai ta fara aikin rigakafin ta ne a ranar 27 ga Disamba, wanda ya kamata ta yiwa ma'aikatan lafiya allurar rigakafin ne a karkashin shirin gwamnati.

Amma asibitin likitanci na Warsaw a makon da ya gabata ya ce ya kuma yi wa wasu mutane 18 rigakafin wadanda ake son su yi aiki a matsayin jakadu na kamfen din yada rigakafin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel