Gwamnatin Tarayya za ta raba wa mata 125,000 tallafin kudi N20,000 - Ministar Jin Kai

Gwamnatin Tarayya za ta raba wa mata 125,000 tallafin kudi N20,000 - Ministar Jin Kai

- Ministar jin kai ta bayyana cewa, gwamnati za ta tallafawa mata da kudi N20,000

- Tallafin za a ba da shi ne a jihohi 36 na fadin kasar ciki har da babban birnin tarayya

- Wakilin ministar ya bayyana hake ne a bikin qaddamar da shirin a jihar Kano

Kimanin matan karkara dubu dari da ashirin da biyar a fadin jihohi 36 na tarayyar da kuma Babban Birnin Tarayya (FCT) za su karbi N20,000 kowannensu a matsayin tallafin kudi daga Gwamnatin Tarayya, This Day ta ruwaito.

Ministar jin kai da walwalar jama'a, Sadiya Umar Farouq ne ta bayyana hakan jiya a Kano yayin kaddamar da shirin a jihar.

Game da tallafin kudin a Kano, ta ce kimanin mata 8,000 a duk fadin kananan hukumomin 44 za su ci gajiyar shirin Gwamnatin Tarayya.

KU KARANTA: Da alamun za a je aikin Hajji bana

Gwamnatin Tarayya za ta raba wa mata 125,000 tallafin kudi N20,000 - Ministar Jin Kai
Gwamnatin Tarayya za ta raba wa mata 125,000 tallafin kudi N20,000 - Ministar Jin Kai Hoto: Facebook/Sadiya Umar Faruq
Asali: Facebook

An ambato ta ne a cikin wata sanarwa da Mataimakin Daraktan yada labarai na ma’aikatar ta, Rhoda Iliya ya fitar a Abuja tana cewa “Za a raba tallafin kudi na N20,000 ga mata matalauta kimanin 125,000 a fadin jihohi 36 na tarayyar da kuma Babban Birnin Tarayyar. ”

Farouq, wacce Babban Sakatare na Ma’aikatar, Bashir Alkali ya wakilce ta a wajen taron a Kano, ya ce an bullo da aikin ne a shekarar 2020 domin ci gaba da aiwatar da tsarin zamantakewar gwamnati.

"An tsara shi ne don ba da tallafi sau ɗaya ga wasu mata matalauta da masu rauni a yankunan karkara da yankunan birane a duk faɗin ƙasar"

A cewar ta, ana sa ran tallafin zai kara kudin shiga da kuma dukiya ga wadanda suka ci gajiyar shirin.

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya yaba wa gwamnati kan bullo da shirye-shiryen da suka dace don tallafawa gajiyayyu da marasa karfi a cikin al’umma, musamman mata da yara.

Ya kuma yabawa ma'aikatar saboda shigar da karin mutane 35,000 da suka ci gajiyarta daga majalisun kananan hukumomi 15 karkashin shirin na Canjin Kuɗi.

Gwamnan wanda ya sami wakilcin Mataimakin Gwamnan, Usman Alhaji, ya bukaci Ministan da ya amince da yin rajistar sauran ragowar wadanda suka ci gajiyar su 35,000 daga kananan hukumomin.

KU KARANTA: Ma'aikata sama da 300 ba a biyansu albashi a Majalisar Dokoki

A wani ci gaba makamancin haka, ministar ta jin kai ta bayyana cewa sama da masu cin gajiyar 4,000 a fadin kananan hukumomin 27 na jihar Jigawa za su ci gajiyar tallafin da gwamnatin tarayya ta ba matan karkara a jihar.

A wani labarin, Hukumar lura da wutan lantarkin Najeriya NERC, ta amince da kara farashin wutan lantarki na kashi 50 kan abinda kwastomomi ke biya yanzu a fadin tarayya, rahoto daga Daily Trust.

Hakan zai shafi kamfanonin raba wutan lantarki 11 dake Najeriya.

Wannan na zuwa ne watanni biyu kacal da kara farashin a watan Nuwamba 2020. A cewar umurnin waiwayan farashin shekara-shekara da sabon shugaban NERC, Engr. Sanusi Garba, ya rattaba hannu ranar 30 ga Disamba, 2020, kuma aka gani ranar Talata, an fara dabbaka sabon farashin ne fari daga ranar 1 ga Junairu, 2021.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel