COVID-19: Tashin hankali a Poland
Wani asibiti a Warsaw yana cikin tashin hankali saboda yin allurar rigakafin COVID-19 ga mashahurai da 'yan siyasa, wanda ya haifar da fushin jama'a kuma ya haifar da binciken gwamnati wanda ya fara a ranar Litinin, jaridar The Punch ta ruwaito.
Poland, wacce kamar yawancin kasashen Turai ta fara aikin rigakafin ta ne a ranar 27 ga Disamba, wanda ya kamata ta yiwa ma'aikatan lafiya allurar rigakafin ne a karkashin shirin gwamnati.
KU KARANTA: Babbar Magana: Akwai yiyuwar barkewar sabon yajin aiki a Jami'o'i
Amma asibitin likitanci na Warsaw a makon da ya gabata ya ce ya kuma yi wa wasu mutane 18 rigakafin wadanda ake son su yi aiki a matsayin jakadu na kamfen din yada rigakafin.
Asibitin ya ce ya bayar da jimillar allurai 450, da suka hada da 300 na ma'aikatansa da kuma 132 ga iyalansu da marasa lafiya.
Jerin marasa lafiyar ya hada da wasu ‘yan siyasa.
Daga cikin mashahuran akwai 'yar fim Maria Seweryn, wacce ke da shekaru 45, mawakiya Michal Bajor, mai shekaru 63, da Edward Miszczak, wata' yar jaridar TV mai shekaru 65.
Alurar rigakafin da ba a saba gani ba ta fara bayyana ne lokacin da Leszek Miller, wani dan majalisar dattijai kuma tsohon firai minista mai jinya a asibiti, ya wallafa wani hoto na asibiti da ke nuna ya yi allurar a ranar 30 ga Disamba.
KU KARANTA: Nijeriya ta fi yadda ta kasance muni a shekaru 6 - Jigo a jam'iyyar APC
Wasu 'yan siyasa na gida a wasu sassan Poland, ciki har da membobin jam'iyya mai mulki ta Law and Justice (PiS), suma an soke su sosai kan yin allurar ba kan ka'ida ba.
A wani labarin daban, Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, duk da tabbacin da Gwamnatin Tarayya ke da shi na iya samar da allurar riga-kafin COVID-19 da ake matukar bukata kuma har ma da yin ta kyauta a kan ‘yan Nijeriya, majalisar dattijai da wasu bangarorin‘ yan Nijeriya suna tunanin akasin haka a tsakanin N400bn da aka shirya kashewa.
Kodinetan rundunar tsaro ta kasa (PTF) a kan COVID-19, Dokta Sani Aliyu, a ranar Talata, ya ce allurar rigakafin ta COVID-19, lokacin da Gwamnatin Tarayya ta sayo ta, za a yi wa ‘yan Nijeriya ne kyauta.
Dakta Aliyu ya ce gwamnati na da isasshen shiri kan yadda za a kai da bayar da allurar tare da bayar da tabbacin cewa za a yiwa ‘yan Nijeriya allurar rigakafin. Ya ce, “Jiya shugaban ya ba wa
Firayim Minista Mateusz Morawiecki ya fada wa kamfanin dillancin labarai na PAP a ranar Asabar cewa "bin dokokin jerin allurar rigakafin nuna girmamawa ne ga ka'idojin hadin kan jama'a".
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng