Gwamna Sule ya naɗa mace ta farko alkalin alkalai a Jihar Nasarawa

Gwamna Sule ya naɗa mace ta farko alkalin alkalai a Jihar Nasarawa

- Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya nada Justice Aisha Bashir babbar jojin jihar

- Mai shari'a Aisha Bashir ita ce ta farko mace da ta zama babbar joji tun kafa jihar a shekarar 1996

- Gwamna Sule ya sanar da nadin ta ranar Talata a Lafia, wajen taron karrama tsohon babban jojin jihar da ya yi ritaya

Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya nada Justice Aisha Bashir a matsayin mukaddashin babbar jojin jihar da zata maye gurbin Justice Suleiman Dikko, wanda ya ajiye aiki bayan ya kai shekaru 65 na ajiye aiki, Leadership ta ruwaito.

Gwamnan, wanda ya sanar da nadin a garin Lafia, ranar Alhamis a wani taron karramawa da aka shiryawa tsohon alkalin alkalan, ya ce hakkin sa ne nada alkalin alkalai duk lokacin da bukatar haka ta taso, kuma bukatar ta taso bayan ritayar Justice Dikko.

Gwamna Sule ya nada mace ta farko alkalin alkalai a Nasarawa
Gwamna Sule ya nada mace ta farko alkalin alkalai a Nasarawa. Hoto: @LeadershipNGA
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Abinda yasa na bari wani daban ya yi min ciki a gidan mijina, matar aure

Gwamnan ya roki tsohon jojin da ya ci gaba da bawa bangaren shari'a goyon baya, lokacin da ya ke aika sakon fatan alheri ga babban joji mai ritaya.

A nata bangaren, Aisha Bashir, wanda itace mace ta farko ta zama babbar jojin jihar tun da aka kafa ta a 1996, ta taya babban joji mai ritaya bisa nasarar kammala aikin sa ga jihar ta kuma yi masa fatan alheri a sauran rayuwar sa.

KU KARANTA: Kungiyar kwallon kafa ta Nasarawa United ta bayyana bacewar dan wasan ta

Sabuwar babbar jojin ta roki gwamnati da ta kara albashin bangaren shari'a, don taimaka wajen magance matsaloli da dama, ta na tabbatar da cewa zata yi abin da ya dace, ba tare da tsoro ko alfarma ba, kuma bisa doron doka.

Taron karramawar ya samu halartar manyan lauyoyi, alkalan manyan kotuna, na majistire da manyan alkalan makwabtan jihohin Benue da Plateau da sauran manyan baki.

A wani labarin daban, Sanata Elisha Abbo mai wakiltar mazabar Adamawa Ta Arewa a Majalisa ta 9 ya tabbatar da cewa zai yi takarar gwamna a Jihar Adamawa a shekarar 2023, The Punch ta ruwaito.

Abbo wanda ya bayyana hakan a Ganye kuma ya ce ya fice daga jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ne saboda jam'iyyar ta mutu.

A wurin gasar gano zakarun 'yan kwallon kafa da sashin matasa na kungiyar yakin neman zabensa ta shirya, mai suna Sanata Ishaku Abbo Ambassadors, (SIA Ambassadors), Abbo ya ce zai yi takarar kujerar gwamna a Adamawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel