Kungiyar ƙwallon ƙafa ta Nasarawa United ta bayyana ɓacewar ɗan wasanta

Kungiyar ƙwallon ƙafa ta Nasarawa United ta bayyana ɓacewar ɗan wasanta

- Kungiyar kwallon kafa ta Nasarawa United ta sanar da bacewar dan wasanta Muhammad Hussain

- Shugaban kungiyar na Nasarawa United Isaac Danladi ne ya sanar da haka a ranar Laraba a garin lafiya, babban birnin Jihar Nasarawa

- Kungiyar ta gargadi duk wani mutum ko kungiya da ke shirin dauke dan wasan da ta yi hattara saboda har yanzu yana da ragowar kwantaragi

Hukumar Kungiyar kwallon kafa ta Nasarawa United ta sanar da cewa daya daga cikin yan wasan ta, Muhammad Hussain, ya bace, kuma ba a san inda ya ke ba.

Shugaban kungiyar Nasarawa United, Isaac Danladi ne ya bayyana haka ranar Laraba a garin Lafia, ta kafafen yada labaran kungiyar, The Punch ta ruwaito.

Kungiyar kwallon kafa ta Nasarawa United ta bayyana bacewar dan wasan ta
Kungiyar kwallon kafa ta Nasarawa United ta bayyana bacewar dan wasan ta. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Zamfara: 'Yan bindiga sun kashe dillalin da shanu saboda yaki siyan shanun sata

Danladi ya bayyana cewa dan wasan ya na da ragowar kwantaragi da kungiyar kuma ya na karbar albashin sa duk wata har kawo yanzu, kafin a neme shi a rasa.

Ya kara da cewa Hussain bai dawo kungiyar ba tun barowar su filin atisayen Flying Eagles, bayan cire su daga kofin zakarun Afirka na yan kasa da shekara 20 a kasar Benin a baya bayan nan.

KU KARANTA: Abinda yasa na bari wani daban ya yi min ciki a gidan mijina, matar aure

Shugaban kungiyar ya gargadi duk wani mutum ko wata kungiya da ke shirin dauke dan wasan daga kungiyar da ya yi hattara, ya na mai cewa sun sanar da hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF da kuma hukumar shirya gasar firimiya halin da ake ciki.

A wani labarin daban, Sanata Elisha Abbo mai wakiltar mazabar Adamawa Ta Arewa a Majalisa ta 9 ya tabbatar da cewa zai yi takarar gwamna a Jihar Adamawa a shekarar 2023, The Punch ta ruwaito.

Abbo wanda ya bayyana hakan a Ganye kuma ya ce ya fice daga jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ne saboda jam'iyyar ta mutu.

A wurin gasar gano zakarun 'yan kwallon kafa da sashin matasa na kungiyar yakin neman zabensa ta shirya, mai suna Sanata Ishaku Abbo Ambassadors, (SIA Ambassadors), Abbo ya ce zai yi takarar kujerar gwamna a Adamawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164