Abinda yasa na bari wani daban ya yi min ciki a gidan mijina, matar aure
- Wata mata a Ibadan ta shaidawa kotu yadda ta kwanta da wani saboda mijin ta ba ya haihuwa
- Matar, Toyin Bello ta roki kotu da ta raba aure tsakanin ta da mijin ta saboda rashin haihuwarsa
- Alkalin kotun Henry Agbaje ya raba auren sai dai mijin ya roki a bari su gana da matar
Toyin Bello, wata mazauniyar Ibadan, babban birnin jihar Oyo, ta bada labarin yadda ta sahalewa wani namijin yi mata ciki a gidan mijin ta, The Cable ta ruwaito.
Da ta ke bayani a gaban wata kotun gargajiya a Ibadan ranar Juma'a, Toyin ta bukaci a raba auren shekara 16 tsakanin ta da mijin ta saboda rashin haihuwarsa.
DUBA WANNAN: Gwamnatin Najeriya za ta ceto dan Najeriya da Saudiyya ta yanke wa hukuncin kisa
Toyin ta yi karar mijin na ta a gaban kotu kan yadda ya ke kauracewa kwanciya da ita tsawon shekara 10.
Ta gaya wa kotu cewa sai da tayi ciki da wani daban saboda baza ta iya jure rashin haihuwa ba.
"Na yi ciki da wani don kare miji na daga kunyar rashin haihuwa. Ba ya kwanciya da ni tsawon shekara 10. So ya ke ya kashe ni ma don ya mallaki gida na," a cewar ta.
"Yanzu na bar gidana kuma ina zaune wata coci a unguwar Asi da ke Ibadan. Mai girma mai shari'a, ba zan iya ci gaba da bata lokaci da Dotun ba, shekaru daɗa tafiya suke, dan Allah ka raba auren mu."
KU KARANTA:
Henry Agbaje, shugaban kotun, ya raba auren ya kuma umarci Dotun da ya bar mata gidan ta cikin kwana bakwai.
Ya kuma ce duk wani yunkurin kawo rashin zaman lafiya zai zama babban laifi.
Sai dai, Dotun ya kalubalanci karar, tare da rokon kotun da ta bari ya gana da matarsa.
"Na yadda bani da lafiya har ya hanani samun yaya. Ita ma tana rufe ni a waje ta shige daki," a fadar sa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng