Allah ya yi wa tsohon dan majalisar tarayya daga Kano rasuwa

Allah ya yi wa tsohon dan majalisar tarayya daga Kano rasuwa

- Allah ya yi tsohon dan majalisar tarayya, Alhaji Danlami Hamza rasuwa daga jihar Kano

- Tsohon dan majalisar tarayyar da ya taba wakiltar Fagge, ya rasu sakamakon cutar korona

- An tabbatar da kwantar da shi a Kwanar Dawaki a ranar Asabar inda ya rasu a ranar Lahadi

Tsohon dan majalisar wakilai daga Fagge a jihar Kano, Alhaji Danlami Hamza, ya rasu sakamakon muguwar annobar korona da ta kama shi, The Punch ta ruwaito.

Hamza, wanda aka kwantar da shi a asibiti a ranar Asabar a cibiyar killacewa da ke Kwanar Dawaki a Kano, ya rasu a ranar Lahadi.

Wani makwabcin mamacin mai suna Hassan Ibrahim, ya ce tsohon dan majalisar ya rasu yana da shekaru 70 a duniya.

Allah ya yi wa tsohon dan majalisar tarayya daga Kano rasuwa
Allah ya yi wa tsohon dan majalisar tarayya daga Kano rasuwa. Hoto daga @Vanguardngrnews
Source: Twitter

KU KARANTA: Babu shakka Najeriya za ta tarwatse matukar ba a dauka wannan matakin ba, Fitaccen shugaba a Arewa

Kamar yadda yace, an yi jana'izarsa wurin karfe 6 na yamma a Fagge da ke tsakiyar birnin Kano inda gawar ke cikin motar asibiti da ta kawo shi gida.

Daga bisani, an birne mamacin a makabartar mayanka da ke Fagge tare da taimakon masana kiwon lafiya wadanda suka yi amfani da kayan kariya.

Tsohon dan majalisar ya taba wakiltar mazabar Fagge a majalisar wakilai tsakanin 1999 da 2011 a karkashin jam'iyyar APP.

Ya sake neman kujerar dan majalisa Aminu Goro a 2015 inda ya sha mugun kaye.

KU KARANTA: Daruruwan mazauna kauyukan Borno sun koma gida baya gigita su da Boko Haram tayi a jajiberin Kirsimeti

A wani labari na daban, Bill Gates, daya daga cikin shugabannin gidauniyar Bill da Melinda Gates (BMGF), ya ce har yanzu duniya ta kasa fahimtar dalilin da yasa masu korona a Afrika suka kasa yawa, The Cable ta wallafa.

Mai taimakon jama'an kuma dan Amurkan wanda yake saka hannayen jari a fannin lafiya ya ce, ya yi farin ciki da rashin hauhawar masu cutar a Afrika kamar yadda aka yi hasashe.

"Abu daya da nake farin ciki da rashin faruwar shine rashin tsanantar hauhawar cutar korona a kasashe masu tasowa," ya rubuta a jawabinsa na karshen shekara.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel