Bill Gates: Har yanzu mun rasa dalilin da yasa Korona bata tsananta a Afrika ba

Bill Gates: Har yanzu mun rasa dalilin da yasa Korona bata tsananta a Afrika ba

- Babban mai arzikin nan na duniya, Bill Gates, ya ce har yanzu duniya ta rasa dalilin da yasa korona bata yi kamari a Afrika ba

- Mashahurin mai kudin ya ce hakan yasa shi farin ciki domin hasashen da suka yi bai zamo gaskiya ba game da kasashen masu tasowa

- Ya ce ko a kasar Afrika ta Kudi da cutar ta fi kamari, babu rabin yawan masu cutar da mace-mace kamar Amurka

Bill Gates, daya daga cikin shugabannin gidauniyar Bill da Melinda Gates (BMGF), ya ce har yanzu duniya ta kasa fahimtar dalilin da yasa masu korona a Afrika suka kasa yawa, The Cable ta wallafa.

Mai taimakon jama'an kuma dan Amurkan wanda yake saka hannayen jari a fannin lafiya ya ce, ya yi farin ciki da rashin hauhawar masu cutar a Afrika kamar yadda aka yi hasashe.

"Abu daya da nake farin ciki da rashin faruwar shine rashin tsanantar hauhawar cutar korona a kasashe masu tasowa," ya rubuta a jawabinsa na karshen shekara.

KU KARANTA: Budurwa ta yi watsi da saurayinta bayan ya dauki nauyin karatun ta a kasar waje

Bill Gates: Har yanzu mun rasa dalilin da yasa Korona bata tsananta a Afrika ba
Bill Gates: Har yanzu mun rasa dalilin da yasa Korona bata tsananta a Afrika ba. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

"A halin yanzu, bai zama gaskiya ba hasashen. A kasashen Afrika, yawan masu kamuwa da cutar da mutuwar da ake saboda cutar bai kai Amurka ko Turai ba.

"Kasar da ta fi jin jiki a nahiyar ita ce kasar AFrika ta Kudu, amma ko a can din kasar bata kai Amurka ba da kashi 40 kuma yawan wadanda suka mutu basu kai kashi 50 na Amurka ba."

KU KARANTA: Buhari ya bayyana halin da yake shiga duk lokacin da 'yan ta'adda suka kai hari

A wani labari na daban, ba kamar yadda aka saba ganin sojoji ba, Shugaban kasan Muhammadu Buhari ya kasance mutum mai barkwanci wanda a dukllokacin da yake tattare da mutane ba a zama cikin kunci.

Wani tsohon bidiyo mai ban dariya da ya bayyana a kafar sada zumuntar zamani ya nuna yadda shugaban kasan da wadanda ke zagaye da shi suka fada nishadi.

Akwai yuwuwar a lokacin da Buhari ya hau mulkin kasar karon farko ne aka yi bidiyon. Wani Francis Ekpenyong, mataimaki na musamman a ofishin Yemi Osinbajo ya wallafa a Twitter a ranar 25 ga watan Disamba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel