Babu shakka Najeriya za ta tarwatse matukar ba a dauka wannan matakin ba, Fitaccen shugaba a Arewa

Babu shakka Najeriya za ta tarwatse matukar ba a dauka wannan matakin ba, Fitaccen shugaba a Arewa

- Shugaba a yankin tsakiyar kasar nan, Farfesa Yusuf Turaki, ya ce Najeriya tana dab da tarwatsewa

- Farfesan arewacin Najeriyan ya ce har sai an gyara kundin tsarin mulkin kasar nan ne za a gujewa hakan

- Turaki ya jajanta tsanantar rashin tsaro da ya addabi dukkan kasar nan da yadda hakan ke kamari

Farfesa Yusuf Turaki ya ja kunne inda yace akwai yuwuwar Najeriya ta tarwatse a kowanne lokaci daga yanzu matukar aka cigaba da amfani da kundin tsarin mulkin kasar nan na 1999.

A wata hira da yayi da jaridar The Sun, farfesan ya kwatanta kundin tsarin mulkin kasar nan na 1999 da abinda ba zai kai kasar nan inda ake tsammani ba.

Turaki ya ce babu shakka kundin tsarin mulkin kasar nan yana daga cikin dalilan da suka hana kasar nan cigaba duk da shekaru 60 da tayi da samun 'yancin kai.

KU KARANTA: Miyagu sun halaka mutum 7, sun kone mota dankare da buhunan masara a Kaduna

Babu shakka Najeriya za ta tarwatse matukar ba a dauka wannan matakin ba, Fitaccen shugaba a Arewa
Babu shakka Najeriya za ta tarwatse matukar ba a dauka wannan matakin ba, Fitaccen shugaba a Arewa. Hoto daga Youtube.com
Asali: UGC

Ya ce: "Abinda na gane shine abinda ke faruwa yanzu yana da tushe da babban tarihi wanda aka gina mana tuntuni. Ina tuna tarihin baya, yadda turawan mulkin mallaka suka kafa kasar nan da muke kira da Najeriya.

"A arewacin Najeriya, na yanke shawarar duba bangarori biyu,, na Musulmi da kuma wadanda ba musulmi ba kuma na so duba yadda turawan mulkin mallaka suka gina dokokinsu."

Turaki ya kwatanta kundin tsarin mulkin kasar nan na 1999 da damfara a bayyane, kari da cewa duk wanda yace kundin tsarin mulkin kasar nan na 1999 abun alheri ne ga Najeriya toh son kan shi kawai yake.

KU KARANTA: Budurwa ta yi watsi da saurayinta bayan ya dauki nauyin karatun ta a kasar waje

A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce yana matukar shiga takaici da bakin ciki in har aka samu rashin zaman lafiya da karantsaye a kan tsaro a kasar nan.

Shugaban kasan a sakonsa na Kirsimeti ga 'yan Najeriya ya yi kira garesu da su bada goyon baya ga dakarun soji da sauran hukumomin tsaro.

"Da gangan ba zan ki sauke babban nauyin da ke kaina ba na tabbatar da tsaron rayuka da kadadrori ba. Ina shiga halin takaici matukar aka samu karantsaye a fannin tsaron kasar nan."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel