Daruruwan mazauna kauyukan Borno sun koma gida baya gigita su da Boko Haram tayi a jajiberin Kirsimeti

Daruruwan mazauna kauyukan Borno sun koma gida baya gigita su da Boko Haram tayi a jajiberin Kirsimeti

- Mazauna kauyukan karamar hukumar Hawul da Boko Haram suka ragargaza sun fara komawa gida

- Mayakan ta'addancin sun kai hari kauyukan inda suka kone majami'u biyu a ranar Kirsimeti

- Sun bayyana yadda suka kwana a cikin dajika da tsaunika a yayin gudun ceton ransu yayin harin

Daruruwan mazauna kauyukan Shindifu, Kirbutu, Debiro, Shafffa, Tashan Alade da Azare a karamar hukumar Hawul ta jihar Borno sun fara komawa gidajensu don ganin barnar da 'yan Boko Haram suka yi musu a yammacin Asabar.

Mayakan ta'addancin sun kai hari a lokaci daya yankunan kasa da sa'o'i 48 da suka kai hari garin Garkida da ke jihar Adamawa, Vanguard ta wallafa.

KU KARANTA: Babu shakka Najeriya za ta tarwatse matukar ba a dauka wannan matakin ba, Fitaccen shugaba a Arewa

Daruruwan mazauna kauyukan Borno sun koma gida baya gigita su da Boko Haram tayi a jajiberin Kirsimeti
Daruruwan mazauna kauyukan Borno sun koma gida baya gigita su da Boko Haram tayi a jajiberin Kirsimeti. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

Da yawan mazauna karamar hukumar Hawul Kirisitoci ne kuma tana da nisan a kalla kilomita 200 daga Maiduguri.

A yayin bayyana halin da suka shiga, Mallam James Ishaya, mazaunin garin Shaffa ya ce mayakan ta'addancin sun dauka kusan sa'o'i 10 suna ragargazar jama'a ba tare da dakarun soji sun iso ba.

Ya jajanta yadda da yawa daga cikinsu suka tsere daji inda suka kwana a tsaunika tare da iyalansu kafin su fara komawa gidajensu da safe.

KU KARANTA: Da duminsa: A lokaci daya 'yan Boko Haram suna kai hari a kauyuka 3 na Borno

A wani labari na daban, Bill Gates, daya daga cikin shugabannin gidauniyar Bill da Melinda Gates (BMGF), ya ce har yanzu duniya ta kasa fahimtar dalilin da yasa masu korona a Afrika suka kasa yawa, The Cable ta wallafa.

Mai taimakon jama'an kuma dan Amurkan wanda yake saka hannayen jari a fannin lafiya ya ce, ya yi farin ciki da rashin hauhawar masu cutar a Afrika kamar yadda aka yi hasashe.

"Abu daya da nake farin ciki da rashin faruwar shine rashin tsanantar hauhawar cutar korona a kasashe masu tasowa," ya rubuta a jawabinsa na karshen shekara.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: