Za a yi wa mutane 2 bulala 12 saboda siyar da miyagun kwayoyi a Kano

Za a yi wa mutane 2 bulala 12 saboda siyar da miyagun kwayoyi a Kano

- Kotun majistire karkashin jagorancin mai shari'a mallam Farouk Ibrahim ta zartar hukuncin bulala 12 kan wasu matasa

- Alkalin ya zartar da hukuncin kan Muhammad Sani da Saddam Ali bayan ya same su da laifin siyar da miyagun kwayoyi

- Mai kara Mallam Muhammad Bichi ya ce laifin ya sabawa sashe na 403 na kudin Panel Code

Wata kotun Majistare a ranar Talata ta yankewa mutum biyu, Muhammad Sani, dan shekara 24, da Saddam Ali, mai shekaru 27, hukuncin bulala 12 saboda kama su da laifin siyar da tabar wiwi da wasu miyagun kwayoyi.

Masu laifin, wanda ba a bayyane adireshin su ba, an kama su da laifin mallakar tabar wiwi da kuma wasu kayan maye, Daily Nigerian ta ruwaito.

Za a yi wa mutane 2 bulala 12 saboda siyar da miyagun kwayoyi a Kano
Za a yi wa mutane 2 bulala 12 saboda siyar da miyagun kwayoyi a Kano. Hoto: @daily_nigerian
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Hattara: Yadda za a iya 'sace' bayanan katin ATM din ka

Alkalin kotun, Mallam Farouk Ibrahim, ya tabbatar da laifin su bayan sun karyata zargin mallakar miyagun kwayoyin.

Ibrahim ya umarci ayi musu bulala 12 kowanne bayan sun roki ayi musu sassauci.

Tun da farko, mai kara Mallam Muhammad Bichi, ya fadawa kotu cewa masu laifin sun aikata laifin ranar 21 ga Disamba da misalin 9:00 na dare a Plaza, karamar hukumar Fagge da ke Jihar Kano.

KU KARANTA: Shehu Sani ya shawarci matasan Arewa su kyale Kukah su mayar da hankali kan 'yan bindiga

Bichi ya ce jami'an yan sandan Fagge ne suka kama masu laifin da sacet goma na Rophypnol, wata mummunar kwaya, da dauri daya na tabar wiwi da wani abu mai ruwa ruwa da ake zargin mai bugarwa ne.

Ya ce laifin ya sabawa sashe na 403 na kundin Penal Code.

A wani rahoton da Legit.ng ta wallafa, ministan tsaron Najeriya, Manjo Janar Bashir Salihi Magashi, ya bukaci kiristoci da su yiwa kasa addu'ar zaman lafiya lokacin bukukuwan zagayowar haihuwar Almasihu wato kirsimeti.

Janar Magashi ya mika rokon a sakon taya kiristoci murnar Kirsimeti da ya fitar ranar Alhamis 24 ga watan Disamba kamar yadda Channels Tv ta ruwaito. Kirstimeti: Ku yi wa sojoji addu'a don kawo karshen tashin tsaro, Ministan tsaro.

Ya bukaci kiristoci da su zama kamar Yesu yayin bikin haihuwar tasa ta hanyar kyautatawa yan uwansu yan Najeriya ba tare da la'akari da bambancin addini ba sannan su yi wa kasa addu'ar zaman lafiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel