Hattara: Hanyoyi 4 da zaka iya kare kanka daga masu 'sace' bayanan katin ATM ɗin ka

Hattara: Hanyoyi 4 da zaka iya kare kanka daga masu 'sace' bayanan katin ATM ɗin ka

Yayin da yan Najeriya da dama ke ci gaba da fadawa hannun yan damfara, wasu masana harkar Intanet sunyi bayani kan yadda za a iya satar bayanan katin cirar kudi na ATM.

Sanin wadannan hanyoyin zai iya taimakawa al'umma su kiyayye kansu daga fadawa hannun bata gari masu satar bayannan mutane ko su yaudare su.

Masanan sun bayyana haka a wata hirar da suka yi da jaridar The Nation. A cewar jaridar, ma'aikatan banki sune da alhakin damfara ta hanyar katin ATM.

Masanan sun bayyana hanyoyi daban daban da za a iya diban bayanan ATM din.

1. Za a iya saka wata na'ura a cikin ATM da zata iya daukar bayanan katin ya kuma tura musu daga baya ta yadda za su iya amfani da bayanan sirrin su cire kudi ko sayayya.

Yadda za a iya 'sace' bayanan katin ATM din ka
Yadda za a iya 'sace' bayanan katin ATM din ka. Hoto: rrslagos767
Source: Twitter

2. Mutane suna iya tsayawa a bayan mai amfani da ATM don ganin bayanai. Idan suka samu lamba katin da lambar sirri, za su iya amfani.

3. Mai amfani da PoS zai iya saka katin a cikin na'ura mai kama da injin PoS din amma kuma bayanan kati suke dauka.

4. Yayin siyayya ta yanar gizo wajen shigar da bayanan kati. Wasu lokutan, wasu mutanen na kirkirar shafin karya wajen domin mai siyayya ya shigar da bayansa na sirri da ke kati yayin da su kuma za su kwashe.

Kawai, zai nuna wa mutum "error" wato kuskure ba tare da sanin cewa an debi bayanai kuma za ayi amfani da su ba.

Da suke karin bayani, masanan sun bayyana cewa yawancin damfarar ayyukan barayin yanar gizo ne amma zai matukar wahala kwarrarren masanin intanet ya dinga irin wannan ayyuka ta bayan fage.

A wani rahoton da Legit.ng ta wallafa, ministan tsaron Najeriya, Manjo Janar Bashir Salihi Magashi, ya bukaci kiristoci da su yiwa kasa addu'ar zaman lafiya lokacin bukukuwan zagayowar haihuwar Almasihu wato kirsimeti.

Janar Magashi ya mika rokon a sakon taya kiristoci murnar Kirsimeti da ya fitar ranar Alhamis 24 ga watan Disamba kamar yadda Channels Tv ta ruwaito. Kirstimeti: Ku yi wa sojoji addu'a don kawo karshen tashin tsaro, Ministan tsaro.

Ya bukaci kiristoci da su zama kamar Yesu yayin bikin haihuwar tasa ta hanyar kyautatawa yan uwansu yan Najeriya ba tare da la'akari da bambancin addini ba sannan su yi wa kasa addu'ar zaman lafiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel