Shehu Sani ya shawarci matasan Arewa su kyale Kukah su mayar da hankali kan 'yan bindiga
- Sanata Shehu Sani ya yi wa kungiyar matasan arewa martani kan neman a kama Bishop Mathew Kukah
- Tsohon dan majalisar mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya ya shawarci matasan su mayar da hankali wurin yakar 'yan bindiga su kyale Kukah a Sokoto
- Limamin cocin na Katolika na Sokoto ya zargi Shugaba Muhammadu Buhari da son kai da bangaranci wadda matasan suka ce hakan na iya raba kan kasa
Shehu Sani, tsohon sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ta Tsakiya, ya bukaci matasan Arewa su dena sukar Limamin cocin darikar Katolika na Sokoto, Mathew Kukah, a maimakon hakan su mayar da hankali wurin yakar 'yan bindiga da suka addabi yankin.
A sakonsa na Kirsimeti, Kukah ya zargi gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da nuna son kai. Kukah ya ce Buhari ya sadaukar da burin da Najeriya ke niyyar cimma saboda son kai da fifita yankin Arewa a kan saura.
DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun kashe shugaban 'yan sintiri, sun sace mutane 8 a Katsina
A martaninsu, Hadakar kungiyoyin Arewa, CNG, sun zargi Kukah da kokarin lalata hadin kan kasa ta hanyar tayar da tashin hankali a tsakanin al'umma.
Kazalika, Kungiyar Matasa ta Tuntubar Arewa, AYCF, ta yi kira ayi gaggawar kama Bishop Kukah tare da bincikarsa. Kungiyar ta bayyana kalaman na Kukah a matsayin kira ga sojoji suyi juyin mulki da yi wa gwamnatin demokradiyya bore.
KU KARANTA: Hattara: Yadda za a iya 'sace' bayanan katin ATM din ka
A sakon martanin da ya yi wa matasan na Arewa, Shehu Sani ya ce, "Ya ku matasan Arewa; Ku kyalle Kukah a Sokoto ku yi yaki da 'yan bindigan da ke cikin wandunan ku."
A wani rahoton da Legit.ng ta wallafa, ministan tsaron Najeriya, Manjo Janar Bashir Salihi Magashi, ya bukaci kiristoci da su yi wa kasa addu'ar zaman lafiya lokacin bukukuwan zagayowar haihuwar Almasihu wato kirsimeti.
Janar Magashi ya mika rokon a sakon taya kiristoci murnar Kirsimeti da ya fitar ranar Alhamis 24 ga watan Disamba kamar yadda Channels Tv ta ruwaito. Kirstimeti: Ku yi wa sojoji addu'a don kawo karshen tashin tsaro, Ministan tsaro.
Ya bukaci kiristoci da su zama kamar Yesu yayin bikin haihuwar tasa ta hanyar kyautatawa yan uwansu yan Najeriya ba tare da la'akari da bambancin addini ba sannan su yi wa kasa addu'ar zaman lafiya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng