Kirstimeti: Ku yi wa sojoji addu'a don kawo karshen rashin tsaro, Ministan tsaro

Kirstimeti: Ku yi wa sojoji addu'a don kawo karshen rashin tsaro, Ministan tsaro

Ministan tsaron Najeriya Bashir Salihi Magashi ya bukaci kiristoci da su yiwa rundunonin tsaro addu'a yayin bikin Kirsimeti

- Ministan ya bayyana haka a sakon da ya fitar na taya murnar zagayowar haihuwar Almasihu ranar Alhamis

- Ministan ya ce jam'in tsaro za su ci gaba kokarin kare rayuka don ganin an yi shagulgulan karshen shekara lafiya

Ministan tsaron Najeriya, Manjo Janar Bashir Salihi Magashi, ya bukaci kiristoci da su yiwa kasa addu'ar zaman lafiya lokacin bukukuwan zagayowar haihuwar Almasihu wato kirsimeti.

Janar Magashi ya mika rokon a sakon taya kiristoci murnar Kirsimeti da ya fitar ranar Alhamis 24 ga watan Disamba kamar yadda Channels Tv ta ruwaito.

Kirstimeti: Ku yi wa sojoji addu'a don kawo karshen tashin tsaro, Ministan tsaro
Kirstimeti: Ku yi wa sojoji addu'a don kawo karshen tashin tsaro, Ministan tsaro. Hoto: @MobilePunch
Source: Depositphotos

Ya bukaci kiristoci da su zama kamar Yesu yayin bikin haihuwar tasa ta hanyar kyautatawa yan uwansu yan Najeriya ba tare da la'akari da bambancin addini ba sannan su yi wa kasa addu'ar zaman lafiya.

DUBA WANNAN: Sirrin cin galaba kan 'yan bindiga a Arewa yana Zamfara, in ji Matawalle

Ministan tsaron ya bayyana bukatar zaman lafiya tsakanin mutane, hadin kai da kuma lumana musamman irin wannan lokacin da kasar ke yaki da ayyukan tada kayar baya, yan bindiga da kuma masu garkuwa da mutane da ma wasu munanan ayyuka.

Ya ce akwai bukatar a koma ga Allah ta hanyar addu'o'i don tallafawa jami'ai wajen yakar ayyukan bata gari.

Da yake jinjinawa jami'an sojoji - wanda sakamakon aikin su, wanda aikin su shine tsare rayukan yan kasa, ba zasu su samu damar zuwa yin shagulgulan Kirsimeti cikin iyalan su ba - ya tabbatar musu cewa babban kwamandan jami'an tsaron Najeriya, shugaba Muhammadu Buhari ba zai bar sadaukarwarsu ta tafi a banza.

Janar Magashi ya bayyana cewa hanyar da za a bi don nuna godiya ga jami'an tsaro da suke aiki ba dare ba rana don ganin yan Najeriya sun yi bacci mai dadi (wanda su basa yi) shi ne ayi musu addu'a kuma a dinga sanya idanu a irin wannan lokaci na rashin tsaro.

KU KARANTA: Dakarun soji sun kama gagarumin bokan Gana da 'yan kungiyarsa

Ya godewa jagorancin hukumomin tsaro da kuma manyan hafsoshin tsaro da raguwar jami'ai dama sauran mutane a yunkurin da su kayi kwanan nan wajen cetowa tare da dawo da daliban Kankara, Jihar Katsina.

Ministan ya bayyana nasarar da aka samu wajen ceto yaran a matsayin dakile ayyukan masu garkuwar, ya ce nasarar ita ce babbar kyautar Kirsimeti da karshen shekara ga kasar nan.

Ministan ya umarci jami'an da ke wurare daban daban da su mayar da hankali wajen tsaurara tsaro a fadin kasar; ya kara da cewa jami'an zasu tabbatar da an gudanar da shagulgulan karshen shekara lafiya.

A wani labarin daban, masu garkuwa da da mutane a ranar Laraba sun yi garkuwa da wani dan kasuwa a garin Minjibir, tsawon kilo mita hamsin daga birnin Kano, Daily Nigerian ta ruwaito.

Yan bindigar sun yi dirar mikiya kauyen da misalin karfe 1:00 na dare, suna harbi kan mai uwa da wabi a Masaka da ke kauyen kafin dauke wani dan kasuwa, Abdullahi Kalos.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel