Da duminsa: A lokaci daya 'yan Boko Haram suna kai hari a kauyuka 3 na Borno
- Mayakan ta'addanci Boko Haram sun kai hari kauyuka uku na karamar hukumar Hawul
- Sun isa kauyukan uku da tarin yawansu a lokaci daya inda suka fara harbe-harbe
- An tabbatar da cewa sun kona majami'u 2 sannan mazauna kauyukan sun garzaya daji don tsira
Wasu da ake zargin 'yan Boko Haram ne a halin yanzu suna ragargazar kauyuka uku na karamar hukumar Hawul da ke jihar Borno, majiyoyi suka tabbatarwa Daily Trust.
An gano cewa maharan sun isa da tarin yawansu inda suka kaddamar da harin a kauyukan Tashan Allade, Shaffa da Khiributu dake karamar hukumar Hawul.
Daruruwan mazauna kauyen sun hanzarta barin gidajensu domin neman mafaka bayan sun ji harbe-harben.
KU KARANTA: Bidiyon bawan Allah yana siye lemun mai tsohon ciki tare da bata kyautukan kayan da kudade
An gano cewa mazauna kauyen sun shige dajikan da ke da kusanci da su domin samun mafaka.
Kamar yadda wata majiya daga 'yan sa kai ta sanar, maharan sun kona majami'u biyu a Tashan Allade yayin da mazauna kauyen suke daji.
Wani daga cikin jami'an JTF, Balami Yusuf, ya bayyana cewa maharan suna ta ruwan alburusai a kauyukan Shaffa da Khiributu.
"A halin yanzu da muke magana, suna ta harbe-harbe. Kana iya jin karar. Muna daji kuma mutane tare da kananan yara suna ta kuka. Mun rasa yadda za mu yi," Balami ya koka.
Idan za a tuna, mahara daga kungiyar ta'addancin sun kai hari kauyen Garkida da ke jihar Adamawa wacce ke da makwabtaka da karamar hukumar Hawul a jajiberin Kirsimeti.
Wannan harin ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 6 tare da konewar gidaje masu tarin yawa.
KU KARANTA: Bidiyon lokacin da Buhari ya hadu da sojan da ya fi kowa tsayi a dakarun Najeriya A wani labari na daban, Farfesa Yusuf Turaki ya ja kunne inda yace akwai yuwuwar Najeriya ta tarwatse a kowanne lokaci daga yanzu matukar aka cigaba da amfani da kundin tsarin mulkin kasar nan na 1999.
A wata hira da yayi da jaridar The Sun, farfesan ya kwatanta kundin tsarin mulkin kasar nan na 1999 da abinda ba zai kai kasar nan inda ake tsammani ba.
Turaki ya ce babu shakka kundin tsarin mulkin kasar nan yana daga cikin dalilan da suka hana kasar nan cigaba duk da shekaru 60 da tayi da samun 'yancin kai.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng