Bidiyon bawan Allah yana siye lemun mai tsohon ciki tare da bata kyautukan kayan da kudade

Bidiyon bawan Allah yana siye lemun mai tsohon ciki tare da bata kyautukan kayan da kudade

- Bidiyon wani bawan Allah yana taimakon mata mai tsohon ciki da ke talla ya janyo masa jinjina

- A bidiyon, an ga mutumin yana siye dukkan lemun da matar ke talla kuma yana bata kyautatawa

- A yayin da wasu ke cewa duk riya ce domin an nada bidiyon, wasu na cewa hakan babbar nagarta ce

Ana jajiberin ranar Kirsimeti, wani bidyon bawan Allah da ke taimakon mai siyar da lemu ya cika kafafen sada zumuntar zamani.

Jama'a da dama sun dinga kwarara masa yabo tare da jinjina a kan wannan lamarin da yayi.

Bayan mutumin ya kira mai siyara da lemun, ya karba dukkan lemun da take talla sannan ya juye a bayan motarsa.

A yayin da ya dawo mata da tiren tallan, ya hado mata da sha tara ta arziki na kayan Kirsimeti.

KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan bindiga sun kai wa dakarun soji hari, sun kashe sojojin ruwa 2

Bidiyon bawan Allah yana siye lemun mai tsohon ciki tare da bata kyautukan kayan da kudade
Bidiyon bawan Allah yana siye lemun mai tsohon ciki tare da bata kyautukan kayan da kudade. Hoto daga @Eugeniarinda
Asali: Twitter

KU KARANTA: Buhari ya bayyana halin da yake shiga duk lokacin da 'yan ta'adda suka kai hari

Legit.ng ta tattara wasu daga cikin tsokacin jama'a a wallafar.

Wani ami amfani da suka @KnoxMyambo cewa yayi, "Me zai sa yayi haka a nada a bidiyo."

@callmhe_mickey martaninsa cewa yayi, "A gaban kamara? Daga bidiyon za a iya gane cewa daga nesa aka nade shi. Babu yadda mutumin ya iya balle ya hana nadar shi."

A wani labari na daban, ba kamar yadda aka saba ganin sojoji ba, Shugaban kasan Muhammadu Buhari ya kasance mutum mai barkwanci wanda a dukllokacin da yake tattare da mutane ba a zama cikin kunci.

Wani tsohon bidiyo mai ban dariya da ya bayyana a kafar sada zumuntar zamani ya nuna yadda shugaban kasan da wadanda ke zagaye da shi suka fada nishadi.

Akwai yuwuwar a lokacin da Buhari ya hau mulkin kasar karon farko ne aka yi bidiyon. Wani Francis Ekpenyong, mataimaki na musamman a ofishin Yemi Osinbajo ya wallafa a Twitter a ranar 25 ga watan Disamba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel