Bidiyon lokacin da Buhari ya hadu da sojan da ya fi kowa tsayi a dakarun Najeriya

Bidiyon lokacin da Buhari ya hadu da sojan da ya fi kowa tsayi a dakarun Najeriya

- Bidiyon shugaban kasa Muhammadu Buhari inda ya hadu da sojan da yafi kowa tsayi a sojin Najeriya ya bai wa mutane dariya

- Duk da tsayin shugaban kasan don ana kiransa da Dogo ko a lokacin da yake soja, ya hadu da wanda ya fi shi

- A yayin mika wa sojan lambar yabo, sai da shugaban kasan ya daga kansa, alamu da ke nuna tabbas ya shaida dogo ne

Ba kamar yadda aka saba ganin sojoji ba, Shugaban kasan Muhammadu Buhari ya kasance mutum mai barkwanci wanda a dukllokacin da yake tattare da mutane ba a zama cikin kunci.

Wani tsohon bidiyo mai ban dariya da ya bayyana a kafar sada zumuntar zamani ya nuna yadda shugaban kasan da wadanda ke zagaye da shi suka fada nishadi.

Akwai yuwuwar a lokacin da Buhari ya hau mulkin kasar karon farko ne aka yi bidiyon. Wani Francis Ekpenyong, mataimaki na musamman a ofishin Yemi Osinbajo ya wallafa a Twitter a ranar 25 ga watan Disamba.

Bidiyon lokacin da Buhari ya hadu da sojan da ya fi kowa tsayi a dakarun Najeriya
Bidiyon lokacin da Buhari ya hadu da sojan da ya fi kowa tsayi a dakarun Najeriya. Hoto daga @ekpesfrancis.
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: Dalibai za su yi gagarumar zanga-zanga matukar ASUU suka koma yajin aiki, NANS

A bidiyon mai tsayin dakika 30, shugaban kasan yana filin faretin sojin inda yake mika lambar yabo ga dakarun.

Lamarin ya faru ne lokacin da wani zabgegen soja wanda ake tsammanin ya fi kowanne soja tsawo a dakarun sojin Najeriya ya garzayo karbar lambar yabo.

Buhari da kan shi ana kiran shi Dogo saboda tsayin da yake da shi. A lokacin mika lambar yabon, sai da shugaban kasa ya daga kan shi sama sannan ya mika wa dogon sojan.

KU KARANTA: Rahoto: Yaran makarantan Kankara sun fallasa FG, sun bayyana hanyar da aka bi aka cece su

Wannan lamari kuwa ya janyo dariya tare da cece-kuce daga masu kallo wadanda suka hada da hafsin soja. Domin kuwa hatta sojan sai da ya gane tsayinsa ya girgiza shugaban kasan kafin ya sara masa karon karshe ya koma.

Bidiyon ya matukar janyo cece-kuce a kafar sada zumuntar Twitter.

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce yana matukar shiga takaici da bakin ciki in har aka samu rashin zaman lafiya da karantsaye a kan tsaro a kasar nan.

Shugaban kasan a sakonsa na Kirsimeti ga 'yan Najeriya ya yi kira garesu da su bada goyon baya ga dakarun soji da sauran hukumomin tsaro.

"Da gangan ba zan ki sauke babban nauyin da ke kaina ba na tabbatar da tsaron rayuka da kadadrori ba. Ina shiga halin takaici matukar aka samu karantsaye a fannin tsaron kasar nan."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel