Shugaba Buhari ya bada umurnin hukunta fasinjoji da ke kauracewa gwajin COVID 19

Shugaba Buhari ya bada umurnin hukunta fasinjoji da ke kauracewa gwajin COVID 19

- Shugaba Buhari ya kara wa'adin kwamitin yaki da cutar Coronavirus zuwa watan Mayun 2021 don tunkarar zango na biyu na annobar

- Shugaban ya kuma umarci hukumar shige da fice da kuma kwamitin da su tabbatar da an hukunta duk wanda ya kauracewa gwajin COVID 19 bayan shigowa kasar

- Dangane da bukukuwan karshen shekara, Buhari ya shawarci jama'a su kauracewa taruwa mai yawa da kuma tafiyar da bata zama wajibi ba

Shugaba Muhammadu Buhari ya tsawaita wa'adin kwamitin fadar shugaban kasa kan yaki da cutar COVID-19 da sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ke jagoranta, har zuwa karshen watan Mayu na 2021 a ranar Talata.

Buhari ya sanar da kara wa'adin a tattaunawar da ya yi da mambobin kwamitin lokacin da suka gabatar masa da rahoton karshen shekara a fadar shugaban kasa, Abuja.

Shugaban ya kara wa'adin ne saboda dawowar cutar a karo na biyu.

Shugaba Buhari ya bada umurnin hukunta fasinjoji da ke kauracewa gwajin COVID 19
Shugaba Buhari ya bada umurnin hukunta fasinjoji da ke kauracewa gwajin COVID 19. Hoto: @MobilePunch
Source: Twitter

DUBA WANNAN: 2023: APC na Kano ta yi wa Kwankwaso martani, ta ce 'za mu murde zaben kuma ba abinda zai faru'

Buhari ya kuma umarci kwamitin da kuma hukumar shige da fice da su tabbatar da an hukunta duk wani mai shigowa kasar da ya kauracewa gwajin cutar COVID-19, The Punch ta ruwaito.

Shugaban ya ce, "na dauki karin matakai da za a zartar kamar haka: tsawaita wa'adin kwamitin yaki da cutar Coronavirus har zuwa karshen watan Mayu na shekara mai kamawa ta 2021, tare da magance karuwar cutar da kuma kawo rigakafi.

"Kwamitin zai tsara hanyoyi kan yadda za a kawo tare da fara amfani da rigakafin ta hanyar amfani da hanyoyin lafiya da suka yi aiki a sauran rigakafin da suka gabata.

"Kwamitin zai hada hannu da jihohi don samar da duk kayyakin da suka dace, tare da tilasta yadda za a takaita cutar a inda suke mulki. An sanar da shawarwarin masana kan yadda za a takaita yaduwar cutar.

KU KARANTA: Jam'iyyar PDP a Ondo ta dakatar da jiga-jigan mambobinta biyar

"Kwamitin da kuma hukumar shige da fice ta kasa su tabbatar da duk wani mutum da ya shigo kasar nan kuma ya kauracewa gwajin cutar ya fuskanci hukuncin da ya dace, saboda kaucewa ka'idar lafiya."

Yayin da ake gab da fara shagulgulan karshen shekara, shugaban ya bukaci yan Najeriya da su zama masu sanya ido, da kuma gargadin cewa su kauracewa taruwar jama'a da kuma tafiyar da bata zama dole ba.

A wani rahoton daban, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce duba da girman iyakar Najeriya da Jamhuriyar Nijar, Allah ne kadai zai iya tsare iyakokin yadda ya kamata, Daily Nigerian ta ruwaito.

Da ya ke jawabi yayin karbar bakuncin tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo, wadda ke jagorancin tawagar sa ido kan zabe ta ECOWAS a Nijar, Buhari ya ce zai iya duk mai yiwuwa don kawo zaman lafiya a yankin na Sahel.

A cewar sanarwar da Femi Adesina, mai bawa shugaban kasa shawara na musamman kan labarai, shugaban kasar ya jinjinawa takwararsa na Nijar, Shugaba Muhamadou Issoufou, "don bai yi yunkurin sauya kundin tsarin mulki ba don zarcewa bayan kure wa'adinsa biyu."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel