2023: APC na Kano ta yi wa Kwankwaso martani, ta ce 'za mu murde zaben kuma ba abinda zai faru'

2023: APC na Kano ta yi wa Kwankwaso martani, ta ce 'za mu murde zaben kuma ba abinda zai faru'

- Shugaban jam'iyyar APC na Jihar Kano, Abdullahi Abbas ya mayarwa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso martani

- A baya bayan nan, Kwankwaso ya ce baza su sake yarda a maimata musu 'inconlusive' ba a zaben 2023 kuma sai dai 'a mutu, ko ayi rai'

- A martaninsa, Abbas ya ce jam'iyyar APC za ta 'murde' zaben na 2023 kuma babu abinda zai faru domin a cewarsa gwamnatinsu ne

Shugaban wucin gadi na jam'iyyar APC reshen jihar Kano, Abdullahi Abbas, ya mayarwa tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso martani kan maganganun da ya yi game da zaben gwamna na 2023 da ke tafe.

Idan za a iya tunawa, Kwankwaso ya ce jam'iyyar PDP ba zata sake yarda a maimaita mata abinda ya faru a zaben gwamna na 2019 ba inda aka ce zaben bai kammala ba 'inconclusive' a yayin da dan takararta ke kan gaba da kuri'u 26,655.

2023: Shugaban APC na Kano ya yiwa Kwankwaso martani, ya ce 'za mu murde zaben kuma ba abinda zai faru'
2023: Shugaban APC na Kano ya yiwa Kwankwaso martani, ya ce 'za mu murde zaben kuma ba abinda zai faru'. Hoto: @daily_nigerian
Asali: Twitter

Da ya ke maida martani, shugaban na APC a jihar ya bugi kirgi ya ce jam'iyyar za ta 'murde' zaben gwamna na 2023 kuma babu abinda zai faru, Daily Nigerian ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Zulum ya karrama bataliyar sojin da Boko Haram bata taba galaba a kanta ba (Hotuna)

Mista Abbas yayin da yake yiwa 'yan jam'iyyar jawabi yayin rantsar da kwamitin kula da jam'iyyar na APC a ranar Talata a gidan gwamnati ya kara da cewa jam'iyyar APC zata yi amfani da irin tsarin da tayi amfani da shi wurin 'murde' zaben mazabar Gama.

Har wa yau, Mista Abbas ya kuma shaidawa 'yan jam'iyyar APC cewa kada su raga wa 'yan Kwankwasiyya ko a zahiri ko gidajen rediyo inda ya ce zaben na 2023 bai za su dauke shi da wasa ba.

"Kwankwaso ya ce zaben gwamna na 2023 zai zama 'ko a mutu, ko a yi rai'. Toh, a shirye muke. Ba ragwaye bane mu. Mun shirya wa yakin. Ba mu tsoron mutuwa.

"Ga magoya bayan mu, kada ku raga wa 'yan Kwankwasiyya, idan sun zage ku a rediyo ko a zahiri, kada ku tausaya musu.

KU KARANTA: Yan bindiga sun sace dagaci da mutum 15 a kauyen Katsina

"Bari in fada muku, zamu murde zaben 2023 kuma babu abinda zai faru. Za mu maimaita abinda muka yi a mazabar Gama idan 2023 ta zo kuma ba abinda zai faru. Wannan lokacin mu ne. Wannan gwamnatin mu ne," in ji Mista Abbas.

A baya, kun ji cewa gwamnatin jihar Zamfara ta ware naira biliyan 1 a kasafin 2021 don ginawa da gyara masallatan juma'a, makarantun islamiyya, makabartu, wuraren wa'azi da sauran harkokin addini.

Kwamishinan harkokin addinan jihar, Sheik Tukur-Jangebe ne ya bayyana haka, lokacin da ya ke zantawa da manema labarai ranar Juma'a bayan gabatar da kasafin ma'aikatar na 2021 ga majalisar dokokin jihar Zamfara.

Jangebe ya shaida cewa gwamnatin Zamfara ta tsara ayyukan ci gaba a karkashin ma'aikatar addinin musulunci a 2021.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164