Jam'iyyar PDP a Ondo ta dakatar da jiga-jigan mambobinta biyar

Jam'iyyar PDP a Ondo ta dakatar da jiga-jigan mambobinta biyar

- Jam'iyyar PDP reshen Jihar Ondo ta dakatar da manyan mambobinta biyar a ranar Talata 22 ga watan Disamba

- Shugabannin jam'iyyar sun ce jiga-jigan nata sun aikata laifukan da suka saba wa kundin tsarin mulkin jam'iyya

- Jam'iyyar ta kuma zargi manyan mabobin nata da yi wa jam'iyyar zagon kasa

- Dakatarwar da aka yi musu zai cigaba da aiki har zuwa lokaciin da jam'iyyar ta dauki matakin karshe kan zargin da ake musu

Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a Jihar Ondo, a ranar Talata, 22 ga watan Disamba ta dakatar da biyar daga cikin jiga-jigan jam'iyyar.

Jiga-jigan jam'iyyar da abin ya shafa sun hada da Oyedele Ibini, Lad Ojomo, Ayo Fadaka, Rasheed Elegbeleye, and Ebenezer Alabi, kamar yadda TVC News ta ruwaito.

Jam'iyyar PDP a Ondo ta dakatar da jiga-jigan mambobinta biyar
Jam'iyyar PDP a Ondo ta dakatar da jiga-jigan mambobinta biyar. Hoto: @OfficialPDP
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 2023: APC na Kano ta yi wa Kwankwaso martani, ta ce 'za mu murde zaben kuma ba abinda zai faru'

A cewar shugabannin jam'iyyar na jihar, an dakatar da jiga-jigan jam'iyyar ne bisa zarginsu da cin amanar jam'iyya da kuma saba dokokin da ke kundin tsarin mulkinta.

KU KARANTA: Zulum ya karrama bataliyar sojin da Boko Haram bata taba galaba a kanta ba (Hotuna)

Kennedy Ikantu Peretei, mai magana da yawun jam'iyyar reshen jihar Ondo, ya ce dakatarwar da aka yi musu zai cigaba da aiki har zuwa lokacin da kwamitin ladabatarwa na jam'iyyar zata zartar da hukunci kan zargin da ake musu.

A baya, kun ji cewa gwamnatin jihar Zamfara ta ware naira biliyan 1 a kasafin 2021 don ginawa da gyara masallatan juma'a, makarantun islamiyya, makabartu, wuraren wa'azi da sauran harkokin addini.

Kwamishinan harkokin addinan jihar, Sheik Tukur-Jangebe ne ya bayyana haka, lokacin da ya ke zantawa da manema labarai ranar Juma'a bayan gabatar da kasafin ma'aikatar na 2021 ga majalisar dokokin jihar Zamfara.

Jangebe ya shaida cewa gwamnatin Zamfara ta tsara ayyukan ci gaba a karkashin ma'aikatar addinin musulunci a 2021.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: