Allah kaɗai zai iya tsare iyakokin Nigeria da Nijar, in ji Buhari

Allah kaɗai zai iya tsare iyakokin Nigeria da Nijar, in ji Buhari

- Muhammadu Buhari, shugaban kasar Najeriya ya ce Allah ne kadai zai iya saka idanu a kan iyakokin Najeriya da Jamhuriyar Nijar

- Shugaban kasar ya ce duk da hakan gwamnatinsa zata yi duk mai yiwuwa domin ganin an samu tsaro da zaman lafiya a yankin na Sahel

- Shugaba Buhari ya yi wannan jawabin ne yayin ganawarsa da tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo a Aso Rock a ranar Talata

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce duba da girman iyakar Najeriya da Jamhuriyar Nijar, Allah ne kadai zai iya tsare iyakokin yadda ya kamata, Daily Nigerian ta ruwaito.

Da ya ke jawabi yayin karbar bakuncin tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo, wadda ke jagorancin tawagar sa ido kan zabe ta ECOWAS a Nijar, Buhari ya ce zai iya duk mai yiwuwa don kawo zaman lafiya a yankin na Sahel.

Allah kadai zai iya tsare iyakokin Nigeria da Nijar, Buhari
Allah kadai zai iya tsare iyakokin Nigeria da Nijar, Buhari. Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Batanci ga Annabi: Kotu ta umurci a sakin Mubarak Bala, ta ce a biya shi diyya

A cewar sanarwar da Femi Adesina, mai bawa shugaban kasa shawara na musamman kan labarai, shugaban kasar ya jinjinawa takwararsa na Nijar, Shugaba Muhamadou Issoufou, "don bai yi yunkurin sauya kundin tsarin mulki ba don zarcewa bayan kure wa'adinsa biyu."

Adesina ya ce ya jiyo Buhari na cewa, "Daga Daura na fito, kilomita kadan ke tsakanin mu da Jamhuriyar Nijar, don haka na dan san wani abu game da kasar. Shugaban kasarsu mai mutunci ne kuma mu kan tuntubi juna sosai. Ba zai wuce tsawon lokacin da kudin tsarin mulki ta diba wa shugabanni ba a kasarsa.

"Kazalika, muna da iyaka mai tsawon kilomita 1,400 wadda Allah ne kadai zai iya kiyaye ta yadda ya dace. Zan yi magana da shugaban kasar in bawa kasarsa gudunmawar mu. Ya zama dole muyi duk abinda zamu iya don kawo tsaro a yankin Sahel don duk zai amfane mu."

KU KARANTA: Buhari ya karbi bakuncin tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo (Hotuna)

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya taya Shugaba Buhari murnar ceto yaran makarantar Kankara da murnar cika shekaru 78 a duniya a makon da ta gabata.

Ya yi alkawarin ECOWAS zata tabbatar anyi zaben adalci cikin zaman lafiya a Jamhuriyar Nijar duk da matsalolin da ake fama da su a kasar, ya kara da cewa ya fara tuntubar masu ruwa da tsaki a harkar.

A baya, kun ji cewa gwamnatin jihar Zamfara ta ware naira biliyan 1 a kasafin 2021 don ginawa da gyara masallatan juma'a, makarantun islamiyya, makabartu, wuraren wa'azi da sauran harkokin addini.

Kwamishinan harkokin addinan jihar, Sheik Tukur-Jangebe ne ya bayyana haka, lokacin da ya ke zantawa da manema labarai ranar Juma'a bayan gabatar da kasafin ma'aikatar na 2021 ga majalisar dokokin jihar Zamfara.

Jangebe ya shaida cewa gwamnatin Zamfara ta tsara ayyukan ci gaba a karkashin ma'aikatar addinin musulunci a 2021.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel