Da duminsa: Kotun shari'a ta bada umarnin damko mawakin Buhari, Dauda Kahutu Rarara

Da duminsa: Kotun shari'a ta bada umarnin damko mawakin Buhari, Dauda Kahutu Rarara

- Wata kotun addinin Musulunci da ke zama a Kano ta bukaci da a cukuikuyo mata Dauda Rarara

- Alkali Ibrahim Sarkin Yola ya bada umarnin ne a kan rashin bayyanar mawakin a gaban kotu

- Ana zarginsa da saka wata matar aure a bidiyonsa na wakar siyasa mai taken Jihata

Wata kotun Musulunci da ke zama a jihar Kano ta bada umarnin damko fitaccen mawakin shugaban kasa Buhari, Dauda Kahutu Rarara.

Alkali Ibrahim Sarki Yola wanda yake shugabantar shari'ar, ya bayar da umarnin damko fitaccen mawakin sakamakon rashin bayyanarsa a gaban kuliya don kare kansa daga zargin da ake masa.

Tun dai daga farko, alkalin ya aika wa mawakin sammaci tare da bukatar ya bayyana a ranar 22 ga watan Disamban 2020.

Da duminsa: Kotun shari'a ta bada umarnin damko mawakin Buhari, Dauda Kahutu Rarara
Da duminsa: Kotun shari'a ta bada umarnin damko mawakin Buhari, Dauda Kahutu Rarara. Hoto daga @daily_trust
Source: Twitter

KU KARANTA: SGF: 'Ya'yana 4 ne suka harbu da muguwar cutar korona

Ana tuhumarsa da boye wata matar aure ba bisa ka'ida ba. Wani mutum mai suna Abdulkadir Inuwa ne ya kai karar mawakin kotun domin neman hakkinsa.

Inuwa yana zargin Dauda Rarara da sanya matarsa ta aure a wani bidiyonsa na wakar siyasa mai taken 'Jihata Jihata ce.'

Ya tabbatar wa da kotun cewa an kwashe tsawon wata daya ba a ga matarsa ba, kwatsam sai ga ta a bidiyon.

A saboda haka yake rokon alkalin da ya bi masa hakkinsa.

KU KARANTA: Zargin handamar kudade: Kotu ta yanke hukuncin karshe a kan sirikin Atiku Abubakar

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Ekiti, Dr. Kayode Fayemi tare da takwarorinsa na jihohin Sokoto da Kebbi sun shiga ganawar sirri da Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina a kan yawaitar garkuwa da jama'a.

Fayemi, wanda shine shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, ya yi bayani ga manema labarai bayan taron da suka yi a gidan gwamnatin Katsina.

Ya yi kira ga takwarorinsa da su dauka salon da za su sa matasa su gujewa aikata laifuka, jaridar The Punch ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel