Zargin handamar kudade: Kotu ta yanke hukuncin karshe a kan sirikin Atiku Abubakar

Zargin handamar kudade: Kotu ta yanke hukuncin karshe a kan sirikin Atiku Abubakar

- Wani alkali da ke zama a babban kotun tarayya da ke Legas ya yi watsi da shari'ar sirikin Atiku

- Alkalin ya bayyana cewa kotun bata da hurumin yanke hukunci saboda an yi laifin ne a Abeukuta

- Ana zargin Abdullahi Babalele, wanda sirikin Atiku ne da harkallar wasu kudi har $140,000

Mai shari'a Chukwujekwu Aneke da ke zama a babbar kotun tarayya da ke Legas a ranar Litinin ya sallami Abdullahi Babalele, sirikin Atiku Abubakar, a kan zarginsa da ake da handamar kudi har $140,000.

Kotun ta yi watsi da karar da hukumar yaki da rashawa tare da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta shigar, sakamakon rashin hurumin kotun na sauraron shari'ar bisa ga duban yankin, Daily Trust ta wallafa.

Ya yanke hukuncin cewa, wannan karar da aka maka wanda ake zargin bai kamata a kai ta har jihar Legas ba domin ana zarginsa da aikatawa ne a garin Abeoukuta da ke jihar Ogun.

Zargin handamar kudade: Kotu ta yanke hukuncin karshe a kan sirikin Atiku Abubakar
Zargin handamar kudade: Kotu ta yanke hukuncin karshe a kan sirikin Atiku Abubakar. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

Alkalin ya dogara da hukuncin kotun koli a wata shari'a tsakanin EFCC da Mohammed Dele Belgore a kan irin haka.

An gurfanar da babalele a shekarar 2018 kuma aka sake gurfanar da shi a ranar 8 ga watan Oktoban 2019.

EFCC ta zargi Babalele da bai wa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo $140,000 bisa umarnin Abubakar wanda ke neman kujerar shugaban kasa a 2019.

Ya musanta aikata abinda ake zarginsa da shi a dukkan zaman da aka yi a kotun.

KU KARANTA: Ku mayar da kudin da kuka karba na gangamin #BringBackOurBoys#, Garba Shehu

A wani labari na daban, bayan kwashe kusan shekara daya da kungiyar malamai masu koyarwa na jam'i'o'i suka yi a gida suna yajin aiki tare da hadin kan cutar korona, gwamnatin Najeriya ta ce tana sa ran malaman za su koma aji a watan Janairun 2021.

Ministan kwadago da aikin yi, Chris Ngige ne ya tabbatar da hakan a ranar Litinin, 21 ga watan Disamba.

Ya tabbatar da cewa sun kai wani mizanin daidaitawa da kungiyar malaman jami'o'in da ya kai kashi 98.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel