SGF: 'Ya'yana 4 ne suka harbu da muguwar cutar korona

SGF: 'Ya'yana 4 ne suka harbu da muguwar cutar korona

- Shugaban kwamitin fadar shugaban kasa na yaki da korona, Boss Mustapha, ya ce 'ya'yansa 4 ke dauke da cutar

- Cike da alhini tare da tashin hankali ya ce dukkan yaransa 4 har da mai shekara 1 ya harbu da cutar

- Ya yi kira ga iyaye da su kiyaye kansu tare da kiyaye ahalinsu da samun muguwar cutar nan ta korona

Boss Mustpha, sakataren gwamnatin tarayya ya ce 'ya'yansa hudu ne suka kamu da muguwar cutar korona, jaridar The Cable ta wallafa.

Mustapha, wanda shine shugaban kwamitin fadar shugaban kasa na yaki da cutar korona, ya sanar da hakan ne a wani bayani da yayi a Abuja a ranar Litinin.

Ya ce daga cikin iyalinsa da cutar ta kama har da yaro mai shekara daya.

Sakataren gwamnatin tarayyan ya killace kansa a makon da ya gabata sakamakon mu'amala da yayi da masu cutar.

SGF: 'Ya'yana 4 ne suka harbu da muguwar cutar korona
SGF: 'Ya'yana 4 ne suka harbu da muguwar cutar korona. Hoto daga @Thecableng
Source: Twitter

KU KARANTA: Ku mayar da kudin da kuka karba na gangamin #BringBackOurBoys#, Garba Shehu

Ya ce a yayin da shi da matarsa suka bayyana basu dauke da cutar, 'ya'yansa a halin yanzu suna jinya.

"A gwajin farko da muka yi, sakamakon ya zo inda mutum 6 a cikin gidana suke da cutar. A gwaji na biyu, an tabbatar da kamuwar wasu mutum uku.

"A tsakanin watan Maris zuwa Nuwamba, mun samu mutum 9 a gidan. Gaskiya lamarin akwai tashin hankali," yace.

KU KARANTA: Neymar: Duba gidansa mai darajar N3.3bn da ke Paris tare da Ferrari din sa me darajar N130m

“Ni da matata bamu dauke da cutar amma akwai wadanda ke gidan da suka kamu da cutar. Na karshen nan akwai tashin hankali. Ban harbu ba amma a gaskiya iyalina sun harbu. Ni mahaifin 'ya'ya hudu ne kuma dukkansu sun kamu.

"Tashin hankalin da kowanne mahaifi zai iya shiga shi nake ciki. Da yawan ku iyaye ne, don haka duk abinda za ku yi domin bai wa kanku da iyalanku kariya ku yi."

A wani labari na daban, Gwamnatin tarayya ta kakaba wasu sabbin dokoki yayin hauhawar yaduwar cutar korona a fadin kasar nan, Channels TV ta wallafa.

Boss Mustapha, wanda shine shugaban kwamitin fadar shugaban kasa na yaki da korona, ya sanar da hakan a ranar Litinin bayan bayanin da yayi ga kwamitin a birnin Abuja.

Ya bayyana cewa wannan umarnin sun fito ne daga mashawarta inda aka mika su ga jihohi a kan a tabbatar da su na tsawo makonni biyar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel