Garkuwa da jama'a: Fayemi, Tambuwal, Bagudu sun shiga ganawar sirri da Masari

Garkuwa da jama'a: Fayemi, Tambuwal, Bagudu sun shiga ganawar sirri da Masari

- Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti tare da takwarorinsa na jihohin Sokoto da Kebbi sun yi ganawar sirri

- SUn samu ganwa da gwamnan jihar Masari, Aminu Masari a gidan gwamnatinsa a kan yawaitar satar jama'a

- Gwamna Kayode ya ce tsanantar rashin tsaro a yankin arewa maso yamma da kasar nan tana tada musu hankali

Gwamnan jihar Ekiti, Dr. Kayode Fayemi tare da takwarorinsa na jihohin Sokoto da Kebbi sun shiga ganawar sirri da Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina a kan yawaitar garkuwa da jama'a.

Fayemi, wanda shine shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, ya yi bayani ga manema labarai bayan taron da suka yi a gidan gwamnatin Katsina.

Ya yi kira ga takwarorinsa da su dauka salon da za su sa matasa su gujewa aikata laifuka, jaridar The Punch ta wallafa.

Garkuwa da jama'a: Fayemi, Tambuwal, Bagudu sun shiga ganawar sirri da Masari
Garkuwa da jama'a: Fayemi, Tambuwal, Bagudu sun shiga ganawar sirri da Masari. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

Gwamnan jihar Ekitin ya ce shi da takwarorinsa duk sun damu da halin da tsaron arewa maso yamma da dukkan kasar nan ke ciki.

KU KARANTA: Da duminsa: FG ta saka sabbin dokokin korona, jerin sunayen wurare 3 da ta rufe

Fayemi ya yi kira ga dukkan takwarotinsa da su tsananta yaki da 'yan bindiga da dukkan laifuka da suka addabi yankin.

KU KARANTA: Zargin handamar kudade: Kotu ta yanke hukuncin karshe a kan sirikin Atiku Abubakar

A wani labari na daban, Boss Mustpha, sakataren gwamnatin tarayya ya ce 'ya'yansa hudu ne suka kamu da muguwar cutar korona, jaridar The Cable ta wallafa.

Mustapha, wanda shine shugaban kwamitin fadar shugaban kasa na yaki da cutar korona, ya sanar da hakan ne a wani bayani da yayi a Abuja a ranar Litinin.

Ya ce daga cikin iyalinsa da cutar ta kama har da yaro mai shekara daya. Sakataren gwamnatin tarayyan ya killace kansa a makon da ya gabata sakamakon mu'amala da yayi da masu cutar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel