Buhari ya karbi bakuncin tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo (Hotuna)

Buhari ya karbi bakuncin tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo (Hotuna)

- Tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo ya kai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari ziyara a Aso Rock da ke Abuja

- Shugabaan kasa Buhari da Namadi Sambo sun shiga ganawar sirri kuma a halin yanzu ba a tabbatar da dalilin ziyarar ba

- Sambo, tsohon gwamnan jihar Kaduna ya rike mukamin mataimakin shugaban kasa ne a karkashin mulkin shugaba tsohon Goodluck Jonathan

Shugaba Muhammadu Buhari da tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Namadi Sambo, sun yi ganawar sirri a fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranar Talata 22 ga watan Disamba.

Hadimin shugaban kasa a bangaren sabbin kafafen watsa labarai, Bashir Ahmad ya bayyana hakan ta shafinsa na Twitter @BashirAhmaad.

Buhari ya karbi bakuncin tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo
Buhari ya karbi bakuncin tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo. Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Buhari ya karbi bakuncin tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo (Hotuna)
Buhari ya karbi bakuncin tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo (Hotuna). Hoto: Sunday Aghaeze
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 2023: Sai dai 'a mutu ko a yi rai' a Kano, ba zamu yarda da 'inconclusive' ba, Kwankwaso

A halin yanzu dai ba a sanar da dalilin ganawarsu ba ko abinda suka tattauna. Namadi Sambo dan jam'iyyar adawa ce Peoples Democratic Party, PDP, ne yayin da Shugaba Buhari dan APC ne.

Buhari ya karbi bakuncin tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo (Hotuna)
Buhari ya karbi bakuncin tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo (Hotuna). Hoto: Sunday Aghaeze
Asali: Twitter

KU KARANTA: Batanci ga Annabi: Kotu ta umurci a sakin Mubarak Bala, ta ce a biya shi diyya

Sambo shine mataimakin shugaban kasa a karkashin mulkin shugaban kasa Goodluck Jonathan. Kafin ya zama shugaban kasa shine gwamnan jihar Kaduna.

A baya, kun ji cewa gwamnatin jihar Zamfara ta ware naira biliyan 1 a kasafin 2021 don ginawa da gyara masallatan juma'a, makarantun islamiyya, makabartu, wuraren wa'azi da sauran harkokin addini.

Kwamishinan harkokin addinan jihar, Sheik Tukur-Jangebe ne ya bayyana haka, lokacin da ya ke zantawa da manema labarai ranar Juma'a bayan gabatar da kasafin ma'aikatar na 2021 ga majalisar dokokin jihar Zamfara.

Jangebe ya shaida cewa gwamnatin Zamfara ta tsara ayyukan ci gaba a karkashin ma'aikatar addinin musulunci a 2021.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164