Batanci ga Annabi: Kotu ta umurci a saki Mubarak Bala, ta ce a biya shi diyya

Batanci ga Annabi: Kotu ta umurci a saki Mubarak Bala, ta ce a biya shi diyya

- Kotu ta bada umurnin sakin, Mubarak Bala, mutumin da ake zargi da yi wa Annabi Muhammad batanci a Facebook

- Yan sanda sun kama Mubarak Bala ne tun a watan Fabrairun 2020 a Kaduna daga bisani aka kai shi Kano inda aka cigaba da tsare shi

- Kotun ta yanke cewa an keta hakokinsa na dan adam saboda tsare shi tsawon lokaci ba tare da bashi damar ganin lauyoyinsa ba kuma ta umurci a biya shi N250,000

Babban kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta bada umurnin sakin Mubarak Bala, wanda ya yi amfanin da shafinsa na Facebook ya wallafa wasu rubutu da ake ganin batanci ne ga Annabi Muhammad (SAW), Daily Trust ta ruwaito.

An kama, Bala, shugaban Humanist Association of Nigeria, a watan Fabrairu a gidansa da ke Kaduna bayan wasu lauyoyi sun shigar da kara a kansa inda suke zargin ya yi wa Annabi Muhammad batanci a shafinsa na Facebook.

Yanzu yanzu: Kotu ta bada umurnin sakin Mubarak Bala, ta ce a biya shi diyya
Yanzu yanzu: Kotu ta bada umurnin sakin Mubarak Bala, ta ce a biya shi diyya. Hoto: Mubarak Bala
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Aisha Buhari ta tafi ganin likitoci ne a Dubai, ba rashin tsaro ya kore ta ba, in ji hadiminta

Yan sandan jihar Kaduna suka kama shi sannan daga bisani aka mayar da shi hannun yan sandan jihar Kano a ranar 2 ga watan Mayun 2020.

Da ya ke yanke hukunci kan korar da lauyoyin Bala suka shigar na zargin keta hakkinsa na bil adama, Mai shari'a Inyang Ekwo ya ce tsare Bala da 'yan sanda suka yi na tsawon watanni ya keta hakkinsa na 'yanci, adalci, zirga-zirga da 'yancin tofa albarkacin bakinsa.

"Rashin barin wanda ake zargi ya gana da lauyoyinsa keta hakkinsa na adalcin shari'a ne da samun lauya kamar yadda ya ke a karkashin sashi na 34 da 35(2) a karkashin kudin tsarin kasa ta 1999."

KU KARANTA: Sule Lamiɗo: PDP ce kaɗai zata iya warware matsalolin Nigeria

Alkalin ya kuma umurci rundunar 'yan sanda su biya naira 250,000 ga wanda ake yin karar.

Mubarak Bala ya dade yana sukar addini tun bayan ridda daga addinin musulunci a shekarar 2014.

An kuma gano cewar iyayensa sun taba kai shi zuwa asibitin kwakwalwa a kan tilas a Kano amma daga bisani aka sako shi kuma tun lokacin ya cigaba da samun barazanar kisa.

A baya, kun ji cewa gwamnatin jihar Zamfara ta ware naira biliyan 1 a kasafin 2021 don ginawa da gyara masallatan juma'a, makarantun islamiyya, makabartu, wuraren wa'azi da sauran harkokin addini.

Kwamishinan harkokin addinan jihar, Sheik Tukur-Jangebe ne ya bayyana haka, lokacin da ya ke zantawa da manema labarai ranar Juma'a bayan gabatar da kasafin ma'aikatar na 2021 ga majalisar dokokin jihar Zamfara.

Jangebe ya shaida cewa gwamnatin Zamfara ta tsara ayyukan ci gaba a karkashin ma'aikatar addinin musulunci a 2021.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164